Shugaban Turkiyya Erdogan ya karɓi baƙuncin Firaministan Pakistan Sharif a Istanbul

Bayan bikin tarbar firaministan wanda aka yi a hukumance, shugabannin biyu sun tafi ƙai tsaye domin tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi ƙasashensu.

Newstimehub

Newstimehub

4 Jul, 2026

9503f8c2d98003355414ffa0937531879ce404bc819568905a0b55752998181d

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a ranar Asabar ya karɓi baƙuncin Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif a Fadar Vahdettin da ke Istanbul.

Bayan bikin tarbar firaministan wanda aka yi a hukumance, shugabannin biyu sun tafi kai tsaye domin tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi ƙasashensu.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, Shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa Ibrahim Kalin, Shugaban Sashen Sadarwa na Turkiyya Burhanettin Duran, da babban mashawarcin shugaban kasa Akif Cagatay Kilic sun halarci tattaunawar wadda aka gudanar ƙofa a rufe.

Bayan ganawar, ana sa ran shugabannin za su gudanar da taro tare da sauran wakilai na ƙasashen biyu.

Erdogan da Sharif za su kuma gudanar da taron manema labarai tare.