Nijeriya da sauran ƙasashen yammacin Afirka huɗu, Côte d’Ivoire da Ghana da Togo da Jamahuriyar Benin sun ƙaddamar da Hukumar Kula da Hanyar Abidjan zuwa Legas a hukumance.
Jaridar Vanguard ta Nijeriya ta ruwaito cewa hukumar ce za ta jagoranci ginawa da kuma kula da babbar hanyar da za ta haɗa manyan cibiyoyin kasuwanci a yankin, wadda kuma za ta ci kuɗi dala biliyan 16.
Hukumar za ta jagoranci kula da hanyar mai nisan kilomita 1,028 da kuma layi shida da aka yi niyyar yi, kuma za ta zama ɗaya daga hanyoyin da suka fi muhimmanci a Yammacin Afirka lokacin da za ta fara aiki a shekerar 2030.
Jamai’ai sun ce an tsara aikin ne domin inganta sauƙin tafiya ta kan iyakoki da rage tsadar jigilar kayayyaki da kuma ƙarfafa haɗin kai a fannin cinikayya a yankin ta ɓangaren tattalin arzikiny yankin teku da ke da yawan hada-hada.
Ana kuma sa ran hanyar za ta faɗaɗa hada-hadar kasuwanci sosai, inda ake kiyasin cewa za ta iya samar da kimanin dala biliyan $16 a kimar cinikayya a faɗin ƙasashen da ke da hannu a lamarin, tare da kimanin dala biliyan $1.3 na kuɗaɗen harajin kan hanya.
Tare da aikin babbar hanyar, gwamnatocin ƙasashen da ke da hannu a aikin suna duba yiyuwar samar da wani layin dogo na jirgin ƙasa mai tsabar gudu a gefenta domin ƙara inganta sufurin mutane da ta kayayyaki a kan hanyar .
Aikin wani ɓangare ne na ƙoƙarin yankin na zurfafa haɗin kai na tattalin arziki da kuma inganta haɗewar abubuwan more rayuwa a faɗin Yammacin Afirka , musamman a yankin gaɓar tekun da ke da yawan cunkosn mutane da kuma yawan hada-hadar tattalin arziki daga Abidjan zuwa Lagos.















