Gwamnatin ƙasar Nijar ta bayyana ranar Lahadi cewa ta fara saka uranium ɗin da kamfanin Somair, ƙarƙashin mallakin Orano na Faransa, ya haƙo – kafin gwamnatin ta mayar da shi mallakin kasar- a kasuwar duniya.
Haƙar uranium a Nijar na cikin muhimman batutuwan jayayya da ke tsakanin gwamnatin da ta amshi mulki a shekarar 2023 da kamfanin Orano, wanda gwamntin Faransa ce ke da kashi 90 cikin 100 na kamfanin kuma ya shafe gomman shekaru yana juya akalar mahaƙan ma’adinan a Nijar.
An bayyana wannan labarin ne a gidal tabalijin na ƙasar Tele Sahel a wani rahoton da aka fitar da yammacin Lahadi inda ka aka ambato kalaman shugabna ƙasar Janar Abdourahamane Tiani.
Rahoton ya ce Tiani ya kama “abin da Nijar ta ke da ‘yancin yi na juya akalar ma’adinata ta hanyar sayarwa ga duk wanda yake son ya siya a ƙarƙashin dokar kasuwa, cikin cikakken ‘yanci.”
Ministan makamashin Rasha, Sergei Tsivilev, dai ya bayyana a cikin watan Juli cewa Moscow na son ta haƙi uranium a Nijar.
Tun lokacin da gwamnatin ta karɓi mulki a juyin mulkin shekarar 2023, Nijar ta koma ga Rasha, wadda ke da rumbum makaman nukiliya mafi girma a duniya, domin tallafa mata wajen yaƙar masu tayar da ƙayar baya da ke iƙirarin jihadi a ƙasar da ke Yammacin Afirka.
Kazalika ta juya wa tsohuwar uwar gijiyarta Faransa baya inda ta zarge ta da taimaka wa ‘yan aware.
A shekarar 2024, Nijar ta ƙwace ikon kamfanin Orano kan muhimman mahaƙar ma’adinai uku nata a ƙasar: Somair da Cominak da kuma Imouraren, waɗanda ke da tarin uranium mafiyawa a duniya.
a hukumance dai kamfanin Orano na da kashi 60 cikin 100 na hannayen jarin ƙananan kamfanonin, kuma ya shigar da wasu ƙararraki domin ya sake samun iko kan mahaƙar ma’adinan.
A shekarar 2022 dai Nijar ce ta samar da kimanin kashi ɗaya cikin huɗu na uranium da aka kai tashoshin nukiliyar Turai, bisa alƙalluma daga hukumar makamashin nukiliya ta Turai Euratom.









