MDD ta yi gargaɗin cewa cutar Ebola na iya jefa kusan mutane miliyan 1 cikin talauci a DRC

Ɓarkewar cutar Ebola na iya sanya Afirka kashe kusan dala biliyan 3.6 tare da barazana ga mutane fiye 300,000, a cewar wakilin UNDP, Damien Mama.

Newstimehub

Newstimehub

1 Jul, 2026

2026 06 16t205953z 1446434402 rc2oula3s616 rtrmadp 3 health ebola congo

Shirin Ci-Gaba na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP) ya yi gargaɗi a ranar Talata cewa ɓarkewar cutar Ebola na iya jefa kusan mutane miliyan ɗaya cikin talauci a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DRC).

Wakilin UNDP, Damien Mama, ya bayyana a wani taron manema labarai na mako-mako na Geneva a Kinsasha cewa bisa alƙaluma mutum shida cikin goma na rayuwa cikin yanayin talauci.

Ya bayyana cewa a wannan makon an tabbatar da mutane fiye da 1.400 da suka kamu da cutar tare da samun mace-mace 350 a DRC da Uganda, kuma ya yi gargaɗin cewa adadin yana ci gaba da ƙaruwa.

Mama ya ce annobar Ebola a DRC ta fi matsalar lafiya ta cikin gida kawai, yana mai jaddada cewa sama da kashi 90 cikin 100 na waɗanda suka kamu da cutar suna kusa da lardin Ituri wanda kuma ake ɗaukarsa a matsayin babbar cibiyar cinikayya tsakanin ƙasashe maƙwabta.

Afirka za ta iya kashe kusan dala biliyan 3.6

Ya yi gargaɗin cewa ɓarkewar cutar na iya sanya Afirka kashe kusan dala biliyan 3.6 tare da barazana ga mutane fiye 300,000 yayin da za ta haifar wa DR Congo asarar dala fiye biliyan 1 da kuma shafar ayyukan yi 55,000 ko da an shawo kanta.

Kazalika Mama ya jaddada cewa hakan na iya rage yawan tattalin arziki na GDP na nahiyar da dala biliyan 2.37.

Haka kuma an soma ganin tasirin hakan a zahiri inda ake samun ƙarancin ayyuka da raguwar hada-hadar kasuwanni da kuma tura iyalai zuwa ga talauci.

Mama ya ce yanayin ya tilasta wa wasu iyalai karya matakan killace kai, wanda hakan ya nuna cewa matakan kariya na lafiya kaɗai ba su isa ba.