Kungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Sahel (AES) ta fara shirye-shiryen tattaunawa da Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta hanyar ƙaddamar da wani taron bita na manyan jami’ai a birnin Ouagadougou na Burkina Faso.
A cewar kafafen yaɗa labarai na Burkina Faso, taron na kwanaki biyu ya haɗa ƙwararru, jami’an diflomasiyya da manyan jami’an gwamnati daga ƙasashen AES guda uku: Burkina Faso, Mali da Nijar.
Ana sa ran mahalarta taron za su mayar da hankali kan samar da wani daftari na musamman wanda zai zama jagora ga ƙungiyar AES wajen tattaunawa da ECOWAS kan muhimman batutuwan yanki da na ƙasa da ƙasa. Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan samar da matsaya guda ta AES kan haɗin kan yanki, zirga-zirgar mutane da kayayyaki cikin ‘yanci, haɗin gwiwar tattalin arziki da kuma tsaron yankin.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin AES da ECOWAS ke ci gaba da sauyawa bayan da ƙasashen Sahel uku suka fice daga ƙungiyar ta ECOWAS tare da kafa ƙungiyarsu ta haɗin gwiwa.
Da yake jawabi a wajen buɗe taron, Sakatare na Dindindin a Ma’aikatar Harkokin Wajen Burkina Faso, Hermann Yirigouin Toé, ya bayyana AES a matsayin wata alama ta farfaɗowar siyasa a nahiyar Afirka.
“A yau, ƙungiyar AES ita ce madubin farfaɗowar siyasar Afirka wadda ta ginu kan haɗin kai, aiki hannu da hannu da kuma kare muradun al’ummominmu,” in ji Toé.
Ana sa ran sakamakon taron zai taimaka wajen tsara yadda AES za ta tunkari duk wata tattaunawa da ECOWAS a nan gaba, yayin da ɓangarorin biyu ke neman hanyoyin magance ƙalubalen da yankin ke fuskanta.















