Japan na shirin sake shigo da danyen man fetur daga Rasha yayin da take fuskantar matsananciyar matsalar makamashi da rikice-rikicen duniya suka haddasa. An ce kamfanin Taiyo Oil ne zai sayo man daga aikin Sakhalin-2 da ke yankin Gabashin Rasha, matakin da ke nuna yadda ƙasar ke ƙoƙarin cike gibin makamashi cikin gaggawa.
Wannan matsalar ta tsananta ne bayan tangardar da aka samu a samar da makamashi a duniya, musamman sakamakon rikicin da ya shafi Iran wanda ya jawo takaita zirga-zirga a mashigar Strait of Hormuz — wuri mai muhimmanci da ke ɗaukar kusan kashi ɗaya bisa biyar na jigilar mai da iskar gas a duniya. Duk da cewa an cimma tsagaita wuta, har yanzu harkar sufuri a yankin ba ta dawo daidai ba.
Aikin Sakhalin-2 wanda kamfanin Gazprom ke jagoranta yana kuma da hannun jari daga Mitsubishi Corporation da Mitsui & Co.. Saboda wannan haɗin gwiwa da aka dade ana yi, wannan cinikin bai shiga cikin takunkumin da kasashen yamma suka kakabawa Rasha ba sakamakon yaƙin Ukraine.
Jirgin ɗaukar man ya bar tashar a ƙarshen watan Afrilu, kuma ana sa ran zai isa yankin Ehime Prefecture nan ba da jimawa ba, abin da ke nuna gaggawar Japan wajen tabbatar da samun isasshen makamashi.
Matakin na Japan ya nuna yadda rikice-rikicen duniya ke sauya dabarun samar da makamashi, musamman ga ƙasashen da suka dogara sosai da shigo da mai daga waje.
MAJIYAR LABARI: NEWSTIMEHUB














