Hukumomin Faransa sun sanar da kama mutane 135 a faɗin ƙasar a ranar Asabar, yayin da ’yansanda suka yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye a birnin Lyon, tare da tsawaita dokar hana yara ƙanana fita da dare ba tare da rakiyar manya ba a wasu biranen arewacin ƙasar, kamar yadda gidan talabijin na BFMTV ya ruwaito.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Laurent Nunez, ya ce zuwa ƙarfe 1 na rana agogon ƙasar, wato ƙarfe 11 na safe agogon GMT, hukumomi sun kama mutane 135 a sassa daban-daban na ƙasar.
Zanga-zangar da ake gudanarwa a Faransa ta samo asali ne daga fushin jama’a kan ƙaruwar tsadar rayuwa, ƙaruwar farashin kayayyaki da kuma rashin isassun kuɗaɗen gudanar da ayyukan hidimar jama’a, musamman a ɓangaren ilimi.
An fara aiwatar da dokar hana yara ƙanana fita da dare ba tare da rakiyar manya ba a Lille, Denain, Douai da Wattignies. A cewar wata sanarwa ta hukuma daga yankin, an tsawaita dokar har zuwa safiyar Litinin, tare da faɗaɗa ta zuwa Marly da Valenciennes.
Dokar ta shafi wasu yankuna da aka ware, ciki har da manyan sassan tsakiyar birnin Lille. Ta hana yara ƙanana fita waje ba tare da rakiyar manya ba tsakanin ƙarfe 8 na dare da ƙarfe 6 na safe agogon ƙasar.
A birnin Lyon, ’yansanda sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa taron mutane kusan 150 da suka taru kusa da Jami’ar Lyon 3, kamar yadda BFMTV ta ruwaito.
Taron, wanda galibin mahalartansa matasa ne, ya ɗauki kusan mintuna 20 kafin ’yansanda su tarwatsa mahalarta, inda hukumomi suka bayyana taron nasu a matsayin wanda aka gudanar ba tare da izini ba.
Hukumomi sun kuma hana gudanar da zanga-zanga a wasu sassan Lyon, saboda fargabar ɓarkewar ƙarin tarzoma.
A Grenoble, wasu mutane da suka yi ƙoƙarin toshe babbar hanyar mota ta A480 sun haddasa karo tsakanin motoci biyu, lamarin da ya jikkata mutane biyu, sai dai raunin nasu ba mai tsanani ba ne, a cewar gidan talabijin ɗin.
A halin da ake ciki, ’yansanda a birnin Paris sun gudanar da binciken tsaro 635 domin hana yiwuwar tayar da tarzoma.
Hukumomi sun ce jami’an tsaro sun ƙwace wasu kayayyaki, ciki har da wuƙa, da injin yankan ƙarfe na hannu da kuma kayan kariya waɗanda suka haɗa da abin rufe fuska mai tace iska da tabarau na nutsewa ƙarƙashin ruwa.
Hukumomi a Montpellier, Nancy, Caen da Annecy sun kuma ƙi amincewa da buƙatun gudanar da zanga-zanga a waɗannan biranen.















