Ministan Bunkasa Kiwon Dabbobi na Nijeriya, Idi Mukhtar Maiha ne ya bayyana hakan a ranar Talata bayan ya yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu jawabi a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Ya bayyana jihohin Binuwe, da Filato, da Nasarawa, da Kaduna da Adamawa, da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, a matsayin wuraren da suka fi muhimmanci saboda tarihin rikice-rikicen manoma da makiyaya da ake samu, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito.
Maiha ya ce gwamnati ta gano birtalai da ake kiwo guda 417 a duk faɗin ƙasar, kuma ta fara wani shiri na gwaji a Jihar Filato don gwada sabon tsarin samar da wajen killace dabbobi da nufin rage zirga-zirgar shanu.
Ya ce ma’aikatar tana tuntuɓar al’ummomin makiyaya da ƙungiyoyi kimanin 34 don tabbatar da goyon bayansu ga sauyi daga kiwon sake, zuwa kiwon dabbobin da aka tsare a waje guda.
A cewarsa, kwanan nan gwamnati ta gana da makiyaya ƙarƙashin jagorancin Babban Dattijon Kungiyar Miyetti Allah da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, yayin wani taro da aka shirya cikin makonni biyu.
Maiha ya ce kiwon dabbobi da ke yawo ko’ina ya zama tsarin da ba za a iya jurewa ba saboda hanyoyin kiwo sun ɓace sakamakon noma, da bunƙasar birane da haɓaka ababen more rayuwa.
Ya ƙara da cewa, gwamnati za ta haɓaka kiwo don kasuwanci, ta yadda za a bar ciyawa a cikin matsugunan dabbobi ko a girbe ta a wani wuri a kai ta ga dabbobin.
Ministan ya kuma ci gaba da cewa inganta nau’in kiwon zai bai wa makiyaya damar riƙe dabbobi kaɗan amma masu amfani, da rage matsin lamba a ƙasa, yayin da ake ƙara samar da madara da nama, yana mai jaddada yadda tsarin kiwo na zamani na kawo ci-gaba ga al’umma, da haɓaka tattalin arziki, da makarantu, da asibitocin dabbobi, da madatsun ruwa, da asibiton kula da lafiya da ma makamashi mai aiki da hasken rana.












