Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da kwamandan NSCDC bisa mutuwar masu haƙar ma’adinai 37 a jihar Neja

Ibrahim ya ce gwamnatin jihar Neja ta soke gangamin yaƙin neman zaɓe na Jam’iyyar APC da aka shirya yi ranar Asabar, 19 ga watan Satumba, a Minna, babban birnin jihar, biyo bayan aukuwar lamarin.

Newstimehub

Newstimehub

18 Sep, 2026

008d8949 4aad 4608 9a25 0ca20851765e 1789719461796

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta dakatar da kwamandan rundunar tsaro ta NSCDC ta jihar Neja, Suberu Aniviye bayan mutuwar masu haƙar ma’adinai 37 ba bisa ƙa’ida ba a hannun jami’an hukumar.

Ministan harkokin cikin gida na ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana umarnin dakatar da kwamandan ranar Jumma’a inda ya ce an soma gudanar da cikakkaen bincike game da mutuwar mutanen.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Jumma’a, mai ba da shawara na musamman kan watsa labarai ga ministan cikin gidan, Alao Babatunde, ya ambato ministan yana cewa kwamandan zai ci gaba da kasancewa wanda aka dakatar har sai lokacin da aka kammala bincike.

Sanarwar ta ce abin da ya fi damun gwamnatin shi ne kare rayuka, kuma tana aiki domin tabbatar da hakan.

Tunji-Ojo ya yi kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu kuma su bi doka da oda domin ba da damar gudanar da bincike na gaskiya.

Mutum 37 sun mutu

Rundunar NSCDC ta kama mutanen ne a ƙauyukan M.I. Wushishi da Lukotoba na jihar bisa zargin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, amma sun mutu a hannunta.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, kwamandan hukumar NSCDC a jihar Neja, Suberu Aniviye, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a lokacin wani samame da aka kai a ranakun 15 da 16 ga watan Satumba.

Aniviye ya ce, “an samu gomman waɗanda aka kama ɗin a mace da sanyin safiyar ranar Alhamis bayan ɓullar abin da ake zargi tashin gobara ne”.

“Rundunar ta jihar Neja, a ƙoƙarinta na daƙile haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, ta kai samame ranar 15 da 16 ga watan Satumba na shekarar, 2026, inda ta kamo waɗanda ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba,” in ji sanarwar.

“Samamen ya samar da muhimmin sakamako inda aka kama gomman waɗanda ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙ’ida ba da kuma wasu kayayyakin aiki domin a kafa hujja,” in ji kwamandan rundunar.

“Sai dai kuma, da sanyin safiyar ranar 17 ga watan Satumba na shekarar 2026, an samu gomman waɗanda aka kama ɗin a mace, bayan tashin gobara.

“An kai gawarwakin waɗanda ake zargin babban asibitin gwamnati da ke Minna, domin ƙarin bincike don gano musabbabin mutuwarsu.”

Kwamandan NSCDC ya ƙara da cewa rundunar tana aiki da sauran hukumomin tsaro domin gano bakin-zaren.

Ya yi kira ga jama’ar gari da iyalan mamatan su kwantar da hankalinsu kuma su ƙaurace wa matakai da za su iya taɓarɓare doka da oda.

Shi kuwa Gwamnan jihar Neja Umar Bago, ya bayyana a wata sanarwa da sakataren watsa labaransa Bologi Ibrahim, ya fitar, cewa mutum 37 da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba sun mutu a hannun hukumar NSCDC.

Ibrahim ya ce gwamnatin jihar Neja ta soke gangamin yaƙin neman zaɓe na Jam’iyyar APC da aka shirya yi ranar Asabar, 19 ga watan Satumba, a Minna, babban birnin jihar, biyo bayan aukuwar lamarin.

Sakataren watsa labaran ya ce gwamnan ya yi wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa ta’aziyya tare da ayyana kwana uku na zaman makoki domin mutunta mamatan.

NSCDC ta kafa kwamitin bincika mutuwar mutanen a hannunta

Kazalika, Babawale Afolabi, jami’in hulɗa da jama’a na ƙasa na hukumar NSCDC , ya ce babban kwamandan hukumar na ƙasa Ahmed Abubakar, ya ba da umarnin kafa wani kwamitin bincike “mai ƙarfi” game da lamarin.

A wata sanarwa, Afolabi ya ce kwamitin, a ƙarƙashin jagorancin mataimakin babban kwamandan hukumar da ke kula da bayanan sirri da bincike, zai bincika yanayin da ya haddasa aukuwar lamarin nan take.

“An bai wa kwamitin aikin gudanar da cikakken bincike game da yanayin da ya haddasa mace-macen ciki har da yadda waɗanda ake zargin suke a lokacin da aka kama su da lokacin da suka shafe a kulle da yanayin da aka saka suke da irin kiwon lafiyar da aka ba su da sauran yanayin da ke da alaƙa da aukuwar lamarin,” in ji sanarwar.