Ghana ta yi wa jakadanta a Nijeriya kiranye kan zargin maguɗin zaɓe

Matakin ya biyo bayan zarge-zargen sayen ƙuri’u ne yayin zaɓen fid da gwani na ‘yan majalisu a Jam’iyyar NDC.

Newstimehub

Newstimehub

9 Feb, 2026

10a78afc ba58 491e 9b19 6e65f61ec637

Shugaba John Mahama na Ghana ya yi wa jakadan ƙasar a Nijeriya, Baba Ahmed, kiranye bisa zargin hannu a maguɗin zaɓe a zaɓen fid da gwani na ‘yan majalisu a mazaɓar Ayawaso East.

Wata sanarwa da fadar Shugaban ƙasar Ghana ta fitar a Accra ta bayyana cewa an yi Ahmed, wanda ya kasance mai neman takara, kiranye ne sakamakon rawar da ake zargin ya taka a maguɗin zaɓe a matsayinsa na jam’in gwamnati.

Sanarwar ta ce kiranye zai yi aiki ne nan-take, kuma an ɗauki matakin ne domin kauce wa duk wani tunanin rashin adalci ko kuma saɓa wa dokar ɗa’ar ma’aikata ga waɗanda aka bai wa muƙaman siyasa.

cefb9de794dbaa01bda003bd3a56af64e194070b23658fad5e48f7638826251f

Ta jaddada cewa ci gaba da zamansa a ofishin abu ne da ba zai yiwu ba a irin wannan yanayi.

An zargi masu neman takara a zaɓen fid da gwani da laifin sayen ƙuri’u.