Dakarun tsaron Nijar sun daƙile hari a Abalama sun kashe ‘yan bindiga

An kashe biyu daga cikin maharan yayin da aka kama uku daga cikinsu inda ɗaya daga cikin dakarun tsaron ƙasar ya rasu kuma huɗu daga cikinsu suka raunata.

Newstimehub

Newstimehub

5 Sep, 2025

7e753290a5f3f3726752250402ab9ea6720d78a1de464541d3bafafc3a9485d4

Dakarun tsaron Jamhuriyar Nijar sun yi nasarar daƙile hare-hare biyu da ‘yan bindiga suka yi yunƙurin kai wa a sansanonin dakarun tsaron ƙasar da ke garin Abalama a gundumar Aderbissanat.

Kafar watsa labarai ta Actu Nijar ta ruwaito cewa ranar Alhamis ne aka yi bikin gabatar da makaman da dakarun suka ƙwace daga maharan wanda gwamnan yankin Manjo Janar Ibra Boulama Issa, ya halarta.

Sai dai ta ce abin takaici shi ne soja ɗaya ya rasu sannan huɗu sun jikkata a fafatawar da dakarun suka yi da ‘yan bindigar a ranar Talata, ko da yake su ma sojoji sun kashe ‘yan bindiga biyu.

Haka kuma an kama uku daga cikin maharan, yayin da wasu suka tsere ɗauke da muggan raunuka.

Bikin, wanda aka yi a sansanin dakarun tsaron ƙasa na Agadez, ya haɗa jami’ai na farar-hula da soji ciki har da shugaban gundumar Aderbissanat, wanda bai jima da dawowa daga bin maharan ba, da mataimakin shugaban gundumar Agadez da kuma kwamandan bataliya Assarid Almoustapha.