Minsitan Ma’adanai na Nijeriya, Dele Alake ya gargaɗi masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba su “daina kashe kansu” ta hanyar haƙar ma’adanai daga ramukan da aka yi watsi da su ba tare da lasisi.
Alake ya ce, akwai ramukan haƙar ma’adanai fiye da 4,000 da aka yi watsi da su a jihar Filato.
Ministan ya bayyana wannan a wata sanarwar da mai taimaka masa ta musamman kan harkar watsa labarai, Lara Owoeye-Wise, ta fitar bayan mutuwar mutum bakwai a wata ruftawar mahaƙar ma’adanai a Kassa, Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ta jihar Filato.
Alake ya yi kira ga masu zuba jari su haɗa-kai da gwamnati domin sake sarrafa irin waɗannan mahaƙar ma’adanan domin yin ayyuka masu riba.
Da yake mayar da martani kan ruftawar wata mahaƙar kuza da aka yi watsi da ita, ministan ya ce da za a iya kaucewa rashin, da a ce masu haƙar ma’aidanai ba bisa ƙa’ida ba sun haɗa wata ƙungiyar taimakon kai-da-kai, kuma sun nemi lasisi daga gwamnati.
Gyaran mahaƙa
Alake ya ce da lasisi zai iya ba su damar cin moriyar horarwa ta ɓangaren horar da ƙananan masu haƙar ma’adanai na ma’aikatar, tare da tabbatar da samun kuɗaɗen shiga akai-akai.
Yayin da yake kira ga ƙananan masu haƙar ma’adanai a faɗin ƙasar su koyi darasi daga baƙin cikin da ruftawar mahaƙar ma’adanan ta haddasa a ƙasar, ministan ya yi wa mutane da gwamnatin jihar Filato jaje game da aukuwar lamarin tare da addu’ar Allah ya jiƙan mamatan.
“Ƙalubalen da ke gaban gwamnatin jihar da ta tarayya shi ne yadda za a mayar da waɗannan mahaƙar mutuwar zuwa cibiyoyi na wadata na murna”, a cewar Alake.
Ya ce gwannati na maraba da masu zuba jari wajen sake sarrafa waɗannan mahaƙar ma’adanan domin ayyuka na makamashi da yawon buɗe-ido da kuma kiwon kifi.
Alake ya ce haɗa kai da ‘yankasuwa ita ce hanyar da ta fi sauri wajen mayar da matattun kadarorin ababen da za su yi amfani, yana mai ƙarawa da cewa ma’aikatar ta gyara wuraren haƙar ma’adinai 59 da aka yi watsi da su kawo yanzu.















