An shirya tattaunawa kusan 370 a birnin Antalya, inda za a duba batutuwa da suka haɗa da zuba jari a makamashin da ake iya sabuntawa, kayayyakin more rayuwar makamashi da sufurin sama mai ɗorewa.
Taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan Sauyin Yanayi, COP31, ya mayar da hankali kan tsaron makamashi da samar da wutar lantarki da sufuri mai ɗorewa a ranar Talata, rana ta biyu ta taron da ake gudanarwa a birnin Antalya na Turkiyya.
An shirya tattaunawa kusan 370 a wannan rana, inda 140 daga cikinsu za su mayar da hankali kan makamashi da sufuri.
Jadawalin taron ya nuna cewa za a tattauna batutuwa da suka haɗa da kayayyakin more rayuwar makamashi, zuba jari a makamashin da ake iya sabuntawa, da kuma sauya sheƙa zuwa hanyoyin sufuri masu tsafta.
Hankali ya karkata kan tsaron makamashi
A ɓangaren Shuɗi, inda ake gudanar da tattaunawar hukuma, manyan jami’ai da ministoci za su tattauna batutuwan da suka shafi haɗin gwiwar makamashi tsakanin Azerbaijan, Kazakhstan da Uzbekistan.
Sauran zaman za su mayar da hankali kan tsaron makamashi, sauyin tsarin makamashi a Ukraine, da ƙalubalen tabbatar da samar da makamashi abin dogaro a yayin rikice-rikicen yankuna.
Samar da kuɗaɗen gudanar da sauyin makamashi da faɗaɗa kayayyakin more rayuwar makamashin da ake iya sabuntawa na daga cikin muhimman batutuwan da za a tattauna.
Motocin lantarki da sufurin sama mai ɗorewa
A ɓangaren Kore, wanda aka buɗe wa baƙi ranar Litinin, ana gudanar da tattaunawa kan sufuri mai ɗorewa, zuba jari a makamashi mai tsafta da kuma rage amfani da makamashin da ke gurɓata muhalli a masana’antu.
Kamfanin Togg na Turkiyya, mai ƙera motocin lantarki, zai gudanar da wani zama mai taken “Sake Tsara Sufuri Mai Ɗorewa”.
Sauran zaman za su mayar da hankali kan man jiragen sama mai ɗorewa, hanyoyin adana makamashi da kuma rawar da ƙirƙirarriyar basira za ta taka wajen samar da tsarin sufuri mai ɗorewa.
Taron, wanda aka buɗe ranar Litinin, ya fara ne da tattaunawa kan abinci, noma da lafiya, tare da halartar masu tsara manufofi, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, kamfanoni da wakilan ƙungiyoyin fararen hula.
Ana gudanar da COP31 daga ranar 9 zuwa 20 ga Nuwamba a Antalya, da nufin ciyar da tattaunawar ƙasa da ƙasa gaba kan rage hayakin da ke gurɓata muhalli, daidaita al’umma da illolin sauyin yanayi da kuma samar da kuɗaɗen yaƙi da sauyin yanayi.















