Erdogan da shugaban Nijar sun tattauna batun tsaro da dangantakar kasashen biyu ta wayar tarho

Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya sake jaddada goyon bayan ƙasarsa ga cikakken ikon Nijar kan yankunanta da kuma tsaron ƙasar, tare da yin alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.

Newstimehub

Newstimehub

10 Nov, 2026

5556e7c8 d76a 4ee9 9602 bae54d02e27d 1794252236851

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, da takwaransa na Nijar, Abdourahamane Tchiani, sun tattauna ta wayar tarho kan dangantakar kasashen biyu da kuma batutuwan da suka shafi yankin.

Hukumar Sadarwa ta Fadar Shugaban Kasar Turkiyya ce ta bayyana hakan.

A yayin tattaunawar da suka yi a ranar Litinin, Erdogan ya ce za a ci gaba da kokari da kuma daukar matakan karfafa dangantakar kasashen biyu a fannoni daban-daban, kamar yadda hukumar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta wallafa a dandalin sada zumunta na NSosyal.

Haka kuma, Erdogan ya sake tabbatar da goyon bayan Turkiyya ga cikakken ikon Nijar kan yankunanta da tsaron kasar, yana mai bayyana shirye-shiryen Ankara na bayar da dukkan taimakon da ya dace domin samar da hanyoyin tattaunawa da karfafa hadin gwiwar yankin.

Bugu da kari, Erdogan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Tchiani da al’ummar Nijar bisa rasuwar mahaifin shugaban kasar a makon da ya wuce.