Shugaban Zambia Hakainde Hichilema ya samu wa’adi na biyu a kan karagar mulki da fiye da ƙuri’u miliyan 2.9, kamar yadda Hukumar Zaɓe ta Zambia ta sanar da sanyin safiyar Talata.
Hichilema, mai shekaru 64, ya doke babban abokin hamayyarsa a zaɓen shugaban ƙasa na ranar Alhamis ɗin da ta gabata, Brian Mundubile na Jam’iyyar National Restoration Party for Unity and Progress (NRPUP), wanda ya samu ƙuri’u miliyan 1.8, inda Hichilema ya samu fiye da adadin kashi 50 cikin 100 da ƙuri’a ɗaya da kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada domin lashe zaɓe.
“Na gode Zambia. Mun ji daɗi matuƙa saboda amanar da muka miƙa wa hannunmu, domin mu riƙe babban ofishin ƙasar kuma mu sake zama bayinku,” in ji Hichilema a wani saƙo da ya wallafa a Facebook jim kaɗan bayan Shugabar Hukumar Zaɓe ta Zambia, Mwanagala Zaloumis, ta ayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a cibiyar zaɓe ta ƙasa da ke Lusaka, babban birnin ƙasar.
Zaloumis ta ce Hichilema ya lashe zaɓen da gagarumin rinjaye, ta yadda sakamakon daga wasu zaɓaɓɓun rumfunan zaɓe da ke cikin sauran ƙananan hukumomin zaɓe biyar daga cikin 226 na ƙasar ba zai iya yin wani gagarumin tasiri kan sakamakon ƙarshe ba.
Titunan Lusaka sun cika da jama’a tun kafin a sanar da nasarar Hichilema, kuma suka ci gaba da kasancewa cikin annashuwa na tsawon lokaci bayan sanarwar, yayin da mutane daga sassa daban-daban na al’umma suka fito kan tituna, suna jure sanyin safiyar domin yin murnar nasarar.
“Mai girma shugaban ƙasa, don Allah ka ci gaba da kasancewa wannan shugaba nagari da ka kasance ga ƙasar nan. Al’ummar Zambia sun sake nuna amincewarsu da imaninsu da jagorancinka,” in ji Collins Maoma, shugaban jam’iyyar da ta tsayar da Hichilema, wato jam’iyyar United Party for National Development (UPND) mai mulki, yayin da yake magana da manema labarai.















