Manoma biyar, maza huɗu da mace ɗaya, sun mutu bayan wani kwale-kwale ya kife a Kogin Kudi, a Ƙaramar Hukumar Katcha ta Jihar Neja da ke arewacin Nijeriya.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a ƙauyen Shaba-Woshi-Kpaya, da ke gundumar Edotsu, a cewar ganau.
Wani mazaunin yankin, Muhammadu Dan-Asabe, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa mutanen suna kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu ne lokacin da kwale-kwalen ya kife.
Daraktan Yaɗa Labarai da Ayyuka na Musamman na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Dr Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce waɗanda abin ya rutsa da su suna tafiya ne daga ƙauyensu zuwa gonakinsu lokacin da kwale-kwalen ya kife.
An bayyana sunayen mamatan da Yahaya Abubakar, Usman Abubakar, Lami Hussaini, Baba Ahmadu da Salihu Aliyu.
Hussaini ya ce an gano gawawwakin mutanen biyar kuma an yi musu jana’iza a ranar Asabar.
Hadarin kwale-kwale ya zama ruwan dare a al’ummomin da ke zaune a bakin koguna, musamman a lokacin damina da noman rani, lokacin da mazauna yankunan ke dogaro da hanyoyin ruwa domin zuwa gonakinsu.















