Shugaban Amurka Donald Trump ya yi maraba da sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro ta haɗin gwiwa ta Makka tasakanin Turkiyya da Pakistan da kuma Saudiyya.
“Na yi matukar farin ciki da ganin cewa daga ƙarshe Saudiyya da Turkiyya da kuma Pakistan sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro ta haɗin gwiwa ta Makka kwanan nan,” kamar yadda Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social.
Trump ya ce yarjejeniyar ta nuna “yadda yankin Gabas ta Tsakiya ke haɗa kai a tare da kuma yadda ƙasashe za su iya kare kansu ta hanya mai matukar ma’ana. Jinjina ga shugabannin ƙasashen uku da aka ambata.
“WANNAN BABBAN MATAKI NE, MAI KYAU, KUMA NA FARKO MAI MUHIMMANCI – JINJINAI!” a cewar Trump.
Ƙudurin dabaru iri ɗaya
Turkiyya da Saudiyya da kuma Pakistan sun sanya hannu kan yarjejeniyar tsaron ne a wani taron ƙasashe uku a da aka gudanar a Makka a ranar 7 ga Agusta, 2026, inda syuka yi alƙawarin ƙarfafa tsaron kasashen su tare da zurfafa haɗin gwiwar tsaro da kuma inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da ma wasu sassan.
Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana yarjejeniyar a matsayin “ƙudurin dabaru iri ɗaya” da ke da nufin mataki bisa ga canjin yanayi na yanki, yana mai ƙari da cewa tsarin dabarun ƙasashen uku ba wai na “ci gaban yau da kullun ba ne”
“Turkiyya na fifita diflomasiyya a ko wanne lokaci fiye da tashin hankali, da tattanawa kan rikici da kuma haɗin gwiwa mai ƙarfi na yanki fiye da rarrabuwar kawuna. A matsayinmu na ƙasa da ke iya magana da dukkan ɓangarori da kuma ɗaukar nauyi kan batutuwa masu matukar wahala idan suka zama dole, za mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa a yankinmu,” in ji shi.
Yarjejeniyar Tsaron Haɗin Gwiwa ta Makkah ta bai wa ƙasashen uku damar ɗaukar mataki kan duk wani hari da aka kai wa ko wanne daga cikinsu a matsayin hari ga kowa, yayin da take kuma zurfafa haɗin gwiwa a kowane fanni na tsaro.
An samar da yarjejeniyar ne daga daɗaɗɗen haɗin kai na Musulunci da kuma muradun dabaru iri ɗaya, sannan ana sa ran yarjejeniyar za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da haɓaka zaman lafiyar yanki da kuma samar da makoma mai aminci ba tare da soma baƙin wani ɓangare daga waje ba.














