Shugaban Chadi Mahamat Idriss Déby ya yi afuwa ga babban abokin hamayyarsa kuma jagoran ‘yan adawa Success Masra, wanda ya shafe fiye da shekara ɗaya a cikin kurku bayan an same shi da laifin tunzura mutane da kuma kasancewa da hannu a kisan kai.
Fadar shugaban ƙasar ce ta bayyana matakin a wata sanarwa, tana mai cewa ta amince da wata buƙatar neman afuwa ne da lauyoyin Masra suka miƙa.
Masra, wanda tsohon Firaminista ne kuma ɗaya daga cikin ‘yan adawa a Chadi da suka fi fice, an yi masa ɗaurin shekara 20 ne tare da tarar kuɗin cefa biliyan ɗaya ($1.77 million) a bara.
Fadar shugaban ƙasar ta ce ana tsammanin za a saki Masra a cikin kwanakin masu zuwa. Za a sake shi tare da wasu ‘yansiyasa takwas da afuwar ta shafa.
Tarar da za a iya aiwatarwa
“Mutanen tara za a sake su da zarar Ma’aikatar Shari’ar ta kammala shirye-shiryen da suka dace a cikin sa’o’i da kwanakin da suke tafe,” in ji fadar shugaban ƙasar.
“Shugaban ƙasa ya yi musu afuwa. Sai dai kuma, afuwar ba ta ɗauke tara ba, waɗanda za a iya aiwatarwa.”
An kama Masra ne a watan Mayun shekarar da ya gabata bisa zargin alaƙa da jerin arangama a kudu maso yammacin Chadi. Hukumomi sun zarge shi da yaɗa saƙonni na ƙiyayya a shafukan sada zumunta kuma suka alaƙanta shi da tashin hankali.
Afuwar na zuwa ne kwanaki bayan Shugaba Déby ya yi alƙawarin sakin wasu mutane da aka samu da laifi a matsayin wani ɓangare na inganta haɗin kan ƙasa da zaman lafiya da sasantawa a ƙasar ta Tsakiyar Afirka.















