Mali ta yi afuwa ga wani dan Faransa ake zargi da yunkurin kitsa juyin mulki a kasar

Gwamnatin riƙon kwarya ta Mali ta yi afuwa ga wani ɗan ƙasar Faransa wanda ke zaune a gidan yari bayan an yanke masa hukuncin ɗauri na shekara 20 bisa zargin ƙulla makircin kifar da gwamnatin ƙasar, kamar yadda hukumomi suka sanar a ranar Alhamis.

Newstimehub

Newstimehub

14 Aug, 2026

e59f7512 e2e3 41b0 ba71 89f53d4f2aee 1786695201523

Gwamnatin riƙon kwarya ta Mali ta yi afuwa ga wani ɗan ƙasar Faransa wanda ke zaune a gidan yari bayan an yanke masa hukuncin ɗauri na shekara 20 bisa zargin ƙulla makircin kifar da gwamnatin ƙasar, kamar yadda hukumomi suka sanar a ranar Alhamis.

An samu Yann Vezilier da laifin yunƙurin hargitsa gwamnatin Shugaba Assimi Goïta a shekarar da ta gabata. Mahukuntan Mali sun zarge shi da yin aiki “a madadin Hukumar Leƙen Asirin Faransa”, tare da wasu manyan hafsoshin soji da kuma sojoji da dama.

“Mai girma Janar na Sojoji Assimi Goïta, Shugaban Rikon Kwarya kuma shugaban ƙasa, ya yi wa Mista Yann Christian Bernard Vezilier, ɗan ƙasar Faransa, afuwa irin ta shugaban ƙasa wanda Kotun Mali ta yanke masa hukuncin shekaru 20 a gidan yari bisa laifin katsalandan a tsaron ƙasar,” in ji wata sanarwa da gwamnatin Mali ta wallafa a shafinta na Facebook.

Hukumomi ba su bayyana dalilin da ya sa aka yanke shawarar yi masa afuwa ba.

‘Kudirin samar da zaman lafiya’

Sanarwar ta kuma yaba wa Janar Assimi Goïta “saboda wannan mataki na yafiya, wanda ya sake nuna ƙudurinsa na samar da zaman lafiya da tattaunawa, da kuma kyawawan ɗabi’un gafara, karɓar baƙi da karamci waɗanda suka shahara a al’adarmu.”

Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ba ta yi wani bayani kan afuwar ba zuwa ranar Alhamis. A baya Paris ta musanta zargin cewa Vezilier yana aiki a Mali a matsayin jami’in leƙen asirin Faransa, tana mai cewa zargin “ba shi da tushe.”

“Wannan matakin afuwa ba ya sauya gaskiyar abubuwan da kotu ta tabbatar bayan shari’ar da aka gudanar, inda aka mutunta dukkan haƙƙoƙin kariya na wanda ake tuhuma. Haka kuma, matakin ya haɗa da fitar da wanda abin ya shafa daga ƙasar nan take,” kamar yadda gwamnatin Mali ta ƙara da cewa.

Mali, wadda tsohuwar ƙasar mulkin mallaka ce ta Faransa, ta shafe shekaru tana fuskantar matsalar tsaro tun daga 2012, sakamakon ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai masu alaƙa da Al-Qaeda da Daesh.

‘A madadin Hukumar Leƙen Asirin Faransa’

A lokacin da aka kama Vezilier tare da gurfanar da shi a gaban kotu, hukumomi sun zarge shi da yin aiki “a madadin hukumar leƙen asirin Faransa, wadda ta tattara shugabannin siyasa, masu ruwa da tsaki a cikin al’umma da jami’an soji” a Mali.

Ƙasar na ci gaba da fuskantar rikicin siyasa da matsalolin tsaro duk da ƙoƙarin gwamnatin da sojoji ke jagoranta na dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A watan Afrilu, Ministan Tsaron Mali ya mutu a wani harin bam da aka kai da wata mota, wanda ake zargin harin kunar bakin-wake ne, a gidansa da ke kusa da babban birnin ƙasar, Bamako.