Meta ya faɗa a ranar Alhamis cewa ya cire shafukan Facebook da Instagram guda 756,000 a Australia da aka tabbatar na yara ne masu shekaru ƙasa da 16.
An cire shafukan Instagram 462,000 da kuma shafukan Facebook 294,000 zuwa ranar 30 ga Yuni, in ji Meta a cikin wata sanarwa.
Australia ce ƙasa ta farko a duniya da ta saka mafi ƙarancin shekarun buɗe shafukan kafafen sada zumunta zuwa 16 a duk faɗin ƙasar, inda ƙa’idojin suka fara aiki a Disamban 2025.
Meta ya ce an cire fiye da shafuka 500,000 a shirye‑shiryen aiwatar da dokar, sannan an ƙara cire wasu shafukan a cikin watannin a suka biyo baya.
Wasu ƙasashe ma na taƙaita damar yara wajen amfani da kafafen sada zumunta. Faransa ta gabatar da haramcin ƙasa baki ɗaya ga masu shekaru ƙasa da 15, yayin da Sifaniya, da Malaysia da wasu ƙasashe ke duba irin waɗannan ƙa’idoji na shekara.
Meta ya ce ana ci gaba da aiwatar da matakin, kuma ana sa ran adadin zai ƙaru.
Kamfanin ya ce yana amfani da fasahar AI wajen nazarin saƙonni, da sharhi, bayanin shafukan da rubutu a kan hotuna don gano alamun cewa mai shafin na iya kasancewa ƙasa da shekaru 16, ciki har da ambaton ranar haihuwa da ajin makaranta.
Meta ya sauƙaƙa hanyoyin da iyaye da sauran masu amfani za su bi wajen kai rahoton asusun da ake zargin na yara ne da shekarunsu ba su kai su fara amfani da shafukan ba, kuma yana amfani da AI wajen nazarin waɗannan rahotanni.
Ya kuma ƙarfafa matakan da aka tsara don hana waɗanda aka cire shafukansu sake ƙirƙirar sabbi, sannan ya sauya matsayin shekarun amfani a manhajojin Apple App Store na Australia zuwa sama da shekaru 16.















