An kori manyan jami’an Hukumar Leken Asirin Isra’ila saboda gaza kifar da gwamnatin Iran

Shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta Isra’ila, Roman Gofman, ya kori shugaban babban ofishin hukumar da na sashen hukumar na Iran, a cewar Channel 12.

Newstimehub

Newstimehub

7 Aug, 2026

f30d9fad 2e6e 4958 90bd 6bb6b769c2d1 1786057407429

Shugaban Hukumar Leƙen Asirin Isra’ila ta Mossad, Roman Gofman, ya kori manyan jami’an hukumar biyu bayan sun kasa aiwatar da wani shiri na kifar da gwamnatin Iran, a cewar kafar watsa labarai ta Isra’ila Channel 12.

Jami’an su ne shugaban babban ofishin hukumar leƙen asiri, wanda aka naɗa watannin da suka gabata, da kuma shugaban sashen hukumar na Iran, a cewar rahoton Channel 12 a ranar Alhamis.

An ƙirƙiro shirin kifar da gwamnatin Iran tare da haɗin gwiwa da Amurka, kana shirin na neman ƙarfafa amfani da ‘yan ƙasar ta Iran tare da goyon bayan ƙungiyoyin adawa domin kawar da gwamnatin ƙasar yayin da Isra’ila da Amurka ke ci gaba da kai hare-hare ta sama a ƙasar.

Kafar watsa labaran, wadda ta yi nuni kan inda aka kwana, ta ce shirin ko dai an gaza aiwatar da shi ko kuma bai samu nasara ba.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa tashar Channel 12 cewa, tun da farko dangantakar Gofman da jami’an biyu ta yi tsami, tana mai ƙari da cewa korar su ta zo ne a daidai lokacin da ake ta samun gagarumin sauyi a shugabancin Mossad da kuma muhimman abubuwan da suka fi ɗaukar hankali, musamman game da Iran.

Kazalika kafar ta ambato rahotanni daga ƙasashen waje da ke cewa shirin ya ƙunshi yanayi na maye gurbin shugabannin Iran da kuma haɗin gwiwa da jami’an Amurka a wani mataki na “bayan kifar da gwamnati”.

Rahoton ya ce, wani shiri na haɗin gwiwa tsakanin Mossad da CIA ya ƙunshi shigar da mayaƙan Kurdawa zuwa Iran tare da tallafin jiragen sama na Amurka da Isra’ila don maye gurbin gwamnatin Iran da wasu muhimman wurare.

Sai dai ba a kai ga cim ma wannan yunƙuri ba, wanda ya kai ga dakatar da shawarar kana a aka hukunta waɗanda ke da hannu cikin gazawarsa, a cewar kafar.

Babu wani martani a hukumance daga Isra’ila nan-take kan batun korar manyan jami’an.

Amincewar Netanyahu

A ranar 13 ga watan Maris ce Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya amince da cewa kifar da gwamnatin Iran zai yi matuƙar wahala, yana mai cewa “babu tabbaci kan ko haka zai faru’’

Amurka da Isra’ila sun ƙaddamar da yaƙi kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, inda suka kashe mutane fiye da 3,000.

Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuaƙ kan sansanonin Amurka a duk faɗin yankin Gabas ta Tsakiya da kuma kan Isra’ila, wanda ya yi sanadiyyar mace-mace daga ɓangarorin biyu.

A ranar 18 ga Yuni, Washington da Tehran suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya kuma suka fara tattaunawa kan cim ma yarjejeniyar ƙarshe kafin tattaunawar ta tsaya cak kan rashin jituwa kan samun tsaro da ‘yancin zirga-zirga ta hanyar Mashigar Hormuz.

Rikici ya sake barkewa a watan da ya wuce bayan da Amurka ta kai sabbin hare-hare a kan Iran, lamarin da ya sa Tehran ta kai hare-haren ramuwar gayya a yankin, ciki har da Jordan da Bahrain da kuma Kuwait.