Ɗaruruwan mutane sun yi hijira daga kudu maso yammacin Nijar saboda hare-haren ‘yanta’adda

Wasu daga cikin mutanen da suka tsira sun tsere zuwa yankin Tahoua da ke kusa da iyakar Nijeriya, yayin da wasu ɗaruruwa suka nemi mafaka a Dogondoutchi, wani babban gari da ke da nisan kusan kilomita 100.

Newstimehub

Newstimehub

3 Aug, 2026

788ddeba 1757 4dbe b9fc fb3c6a18d326 1785747173096

Ɗaruruwan mutane sun tsere daga gidajensu a kudu maso yammacin Nijar bayan jerin hare-haren da aka kai wa ƙauyukansu a tsakiyar watan Yuli, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnati da majiyoyin yankin suka bayyana.

Ba a taɓa samun adadi mai yawa na mutanen da suka yi gudun hijira a yankin na Dosso irin wannan lokaci ba, yankin da ke da iyaka da Nijeriya da Benin.

Yankin kan iyakar ya zama sabon wurin da hare-haren ta’addanci suka ƙaru tun shekarar 2025, bayan ƙungiyoyin da ke da alaƙa da al-Qaeda da kuma ƙungiyar Daesh sun fara kutsawa yankin, a cewar cibiyar sa ido kan rikice-rikice ta ACLED.

Wani jami’i a yankin ya shaida wa AFP cewa an tilasta wa mazauna ƙauyukan tserewa “a daidai lokacin noman damina” sakamakon “jerin hare-haren ta’addanci” da aka kai a tsakiyar watan Yuli.

Wasu daga cikin waɗanda suka tsira sun tsere zuwa yankin Tahoua da ke kusa da iyakar Nijeriya, yayin da wasu ɗaruruwa suka nemi mafaka a Dogondoutchi, wani babban gari da ke da nisan kusan kilomita 100 (mil 60), kamar yadda gidan talbijin na gwamnati ya ruwaito.

“Wadannan hare-hare na farko sun faru ne aƙalla a ƙauyuka uku a ranar 17 ga Yuli, inda suka yi sanadin mutuwa da jikkatar mutane da dama, dukkansu fararen-hula,” kamar yadda wata majiya daga yankin ta shaida wa AFP.

Har yanzu hukumomi ba su fitar da adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata ba.

A ranar Juma’a, gwamnan yankin Dosso, Kanal Bana Alhassane, ya bayyana a gidan talabijin na gwamnati cewa za a ƙara tsaurara matakan tsaro domin bai wa mazauna damar komawa gidajensu da ci gaba da noma.

A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, Nijar na da fiye da mutane 450,000 da suka rasa matsugunansu a cikin ƙasar sakamakon hare-haren ta’addanci.