Gwamnatin Ghana ta amince da shawara ƙara wa’adin mulkin shugaban ƙasa

Shawarar na daga wani ɓangare na shirin gyaran kundin tsarin mulkin Ghana.

Newstimehub

Newstimehub

31 Jul, 2026

9f62aeb8 6b9c 408d 9105 09d0403bfd08 1785489446555

Gwamnatin Ghana ta amince da shawarar ƙara wa’adin shugaban ƙasa daga shekaru huɗu zuwa biyar, in ji ministan shari’a na ƙasar ta Afirka ta Yamma a ranar Alhamis.

Shugaba John Dramani Mahama ya kafa wani kwamiti a bara wanda ya duba kundin tsarin mulkin 1992, kuma ya bayar da shawarwari, gwamnati ta amince da wasu daga cikin su.

Babban Lauya na Ƙasa kuma Ministan Shari’a Dominic Awine ya ce za kuma a tsawaita wa’adin Majalisar Dokoki don ya daidaita da sabon wa’adin shugaban ƙasa.

Gwamnatin ta ce an tsara tsawaita wa’adin shugaban ƙasa ne domin bai wa gwamnatoci ƙarin lokaci wajen gudanar da mulki.

Za a gyara mafi ƙarancin shekarun zama shugaban ƙasa

“Batutuwan karɓar mulki ne suke cinye watannin farko na kowace gwamnati, yayin da shekarar ƙarshe kuma kusan gabaɗaya tana cike ne da harkokin zaɓe,” in ji Awine.

Gwamnatin ta kuma amince da shawarar kwamitin na rage shekarun da ake buƙata don zama ɗan takarar shugaban ƙasa, wanda yanzu yake 40, amma ta mayar da shekarun zuwa 35 maimakon 30 da kwamitin ya ba da shawara.

Gwamnatin ta kuma amince cewa za a ringa gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a makon farko na Nuwamba don tabbatar da isasshiyae tazara tsakanin zaɓen da ranar rantsarwa ta 7 ga Janairu.

Za a kafa wani kwamitin kuma don tsara wasu ƙudurin gyara dokoki guda biyu da ake sa ran za a kammala nan Oktoban 2026.

Kudurin da ya shafi iya wa’adin da shugaba zai iya yi, zai bi ta wasu matakai kafin ya kai ga ƙuri’ar jin ra’ayi ta ƙasa a 2027.

Kafin ƙuri’ar ta jin ra’ayi ta yi nasara, dole aƙalla kashi 40% na masu rajista su fito su jefa ƙuri’a, kuma aƙalla kashi 75% na waɗanda suka jefa ƙuri’a dole su jefa kuri’ar amincewa.