Tawagar majalisar dokokin NATO ta ziyarci kamfanin Baykar mai ƙera jirage marasa matuƙa a Ankara

An yi wa tawagar bayani game da fasahar tsaro ta Baykar da kuma ayyuka na ƙirƙire-ƙirƙire gabannin taron NATO da za a yi a Ankara tsakanin ranar 7 zuwa 8 ta watan Juli.

Newstimehub

Newstimehub

30 Jun, 2026

abf8dec44274390f43fb489a2511f1e2d1ce64fd819c2fe81cd87c6c766d0104

Shugabannin majalisun dokokin da ke halartar taron majalisun dokokin ƙawancen tsaron NATO a Istanbul sun ziyarci cibiyar fasaha ta ƙasa ta kamfanin Baykar ta tunawa da Ozdemir Bayraktar ranar Talata, inda shugaban majalisar dokokin Turkiyya Numan Kurtulmus ya karɓi baƙuncinsu, gabannin taron ƙawancen tsaro ta NATO na mako mai zuwa a Ankara.

Biyo bayan taron da aka yi a fadar Dolmabahce ta Istanbul ranar Litinin, Kurtulmus, tare da shugabannin majalisun dokoki da kuma manyan wakilan majalisyun dokoki daga ƙasashen cikin ƙawancen, sun yi rangadi a cikin cibiyar.

Yayin ziyarar, shugaban Baykar, Selcuk Bayraktar, ya yi jawabi ga tawagar game da ayyukan kamfanin da fasahar tsaro da kuma ayyukan ƙirƙirar da ake kan yi.

Kurtulmus ya kuma gana da Canan Bayraktar, maiɗakin marigayi Ozdemir Bayraktar, wani na gaba-gaba a tsarin fasaharar tsaro na cikin gida na Turkiyya da kuma tsarin jiragen yaƙi mara matuƙa, da kuma mahaifiyar Selcuk Bayraktar, da shugaba da kuma shugaban ɓangaren fasaha na kamfanin fasahar Baykar.

Ziyarar na zuwa ne gabannin taron ƙawancen NATO na ranar 7 zuwa 8 ta watan Juli a Ankara, wanda zai, a karon farko, haɗa da tattaunawa ta masana’antar tsaro a matsayin wani ɓangare na shirinta a hukumance.