Ministan Tsaron Kasa na Turkiyya, Yasar Guler, ya ce taron kolin shugabannin NATO da za a gudanar a Ankara zai zama “muhimmin sauyi” wajen tsara makomar dabarun kawance yayin da yankin ke ƙara fuskantar matsalar tsaro.
“Ba mu dauki taron NATO da za mu karba baki a Ankara a matsayin haduwar shugabanni kawai ba. Muna ganin wannan taro zai zama muhimmin sauyi wanda zai nuna azamar NATO na daidaita kanta da yanayin tsaro mai canzawa kuma zai tsara makomar hanyar dabarunsa,” in ji Guler.
Ministan ya yi wa ‘yan jarida bayani a Brussels bayan halartar taron ministocin tsaro na NATO da taron Kungiyar Tuntuba kan Tsaron Ukraine gabanin taron kolin shugabannin NATO na 7–8 ga Yuli a Ankara.
Guler ya ce tattaunawar ta mayar da hankali kan matsayin hana hari da kariya na NATO, goyon baya ga Ukraine, da sauran kalubalen tsaro.
Ya ce ya sanar da abokan aikinsa game da gudummawar Turkiyya ga NATO a matsayin daya daga cikin kasashen da suka fi bayar da dakaru, ci gaban da ake samu wajen cika alkawarin kashe kudi na tsaro na kungiyar na kashi 5 cikin 100, tallafi ga Ukraine, da shirye‑shiryen taron Ankara.
Masana’antar tsaro da karfin NATO
Guler ya ce barazanar da aka saba da ita a yanzu tana haɗewa da wasu sabbi waɗanda suka haɗa da hare‑haren yanar gizo, ta’addanci, hadarin tsaron makamashi, da rashin kwanciyar hankali na yankuna, wanda ke bukatar NATO ta ƙarfafa dakatarwa ta hadin gwiwa.
Ya jaddada cewa masana’antar tsaron cikin gida ta Turkiyya ba kawai tana taimaka wa tsaron kasa ba, har ma tana kara gudummawa ga kariyar hadin gwiwa ta NATO.
“Tsarinmu na cikin gida da na kasa suna tallafa wa aiki tsakanin abokan kawance kuma suna taimaka wa dakatarwar kungiyar baki daya. Karfin masana’antar tsaro yana nufin karfin dakatarwa da karfin NATO,” in ji shi.
Guler ya kara da cewa Taron Masana’antar Tsaro da za a gudanar a gefen taron Ankara zai karfafa hadin kai tsakanin abokan kawance, yana mai cewa ministocin tsaro uku na NATO sun jaddada muhimmancin fadada hadin gwiwa da masana’antar tsaron Turkiyya a lokacin ganawa.
Matsayin Turkiyya a cikin NATO
Guler ya ce Ankara na sa ran taron zai tabbatar da ka’idar kariyar hadin gwiwa ta NATO da alkawarin Sashe na 5 yayin karfafa abokan kawance su dauki matakai na ainihi kan kashe kudade don tsaro da cim ma buri mai karfi.
Ya bayyana Turkiyya a matsayin kasa ta biyu a NATO dangane da karfin soja, yana cewa kasar na ci gaba da bada gudummawa sosai ga horo, atisayen soja, ayyuka, da ayyukan umarni da iko a fadin kawancen.
Har ila yau ya haskaka kwarewar Ayyukan Sojin Turkiyya wajen yaki da ta’addanci da ayyukan ketare, yana mai cewa Turkiyya na shirin karbar iko da da rundunar ƙawance ta Allied Reaction Force, wanda ya kira “alamar tabbatacciyar amincin Turkiyya da muhimmancin dabarunta a cikin kawancen.”
Ukraine, Bahar Aswad da Gabas ta Tsakiya
Guler ya ce yakin Rasha da Ukraine bai shafi kasashen biyu kadai ba; ya shafi tsaron Turai, tsaron makamashi, hanyoyin kasuwancin duniya, da ajandar NATO.
Ya ce tun farkon yakin Turkiyya ta bi manufa madaidaiciya da ka’ida kuma tana ci gaba da aiwatar da Yarjejeniyar Montreux yayin da take goyon bayan mallakar yankin da hadin kai tsakanin kasashen bakin Tekun Bahar Aswad.
Ya bayyana zaman lafiya a Tekun Bahar Aswad a matsayin “bangare marar rabuwa na tsaron Turai da Atlantika.”
Game da Gabas ta Tsakiya, Guler ya ce abubuwan da ke faruwa a yankin na da tasiri ga tsaron duniya kuma ya yi maraba da yarjejeniyar da aka cimma don kawo karshen rikicin Iran da Amurka.
Ya kuma ce Turkiyya ta shirya tallafa wa ayyukan kawar bama-bamai da aka dasa a Hormuz idan ya zama dole kuma tana nan a shirye don bada gudummawa ga tsaron ruwa da ‘yancin zirga‑zirgar ruwa bisa dokokin kasa da kasa.














