Gwamnatin Nijar ta ce wani hari da aka kai a ranar Alhamis kan filin jirgin saman ƙasar da sansanin sojin sama da ke babban birnin ƙasar, Niamey, ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an tsaro 11 da fararen hula biyu.
A cikin wata sanarwa da gwamnati ta fitar, ta kuma bayyana cewa an kashe maharan 22 a yayin artabun.
Har zuwa yanzu, babu wata ƙungiya ko mutum da ya ɗauki alhakin kai harin.
Yadda abin ya faru
Run da fari da safiyar Alhamis ɗin nan a filin jirgin sama na Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar, aka ji ƙarar harbe-harben bindigogi da dama kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP, watanni da dama bayan wani babban hari da aka kai filin jirgin.
A watan Janairun da ya gabata, an kai wa Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Diori Hamani da ke babban birnin ƙasar wani mummunan hari na ba-zata, wanda ƙungiyar ta’addanci ta EIS ta ɗauki alhakin kaiwa, inda dakarun tsaron Nijar da mayaƙan Rasha da ke ƙawance da su suka fatattaki maharan.
Kafin faruwar hakan, tashe-tashen hankula na ‘yan ta’adda a ƙasar Nijar sun taƙaita ne kawai a wasu sassan ƙasar.
Biyo bayan harin na watan Janairu, hukumomi sun rusa dubban gidajen da aka gina ba bisa ƙa’ida ba a wata unguwa da ke kusa da filin jirgin saman.
Hukumomi sun bayyana cewa ‘yan ta’adda sun mamaye unguwar, inda suka saje da mazaunanta domin ƙaddamar da harin.
Nijar, ƙasa mai faɗin gaske a yankin Sahel na yammacin Afirka, ta kwashe tsawon shekaru goma tana fama da tashe-tashen hankula daga ƙungiyoyin ta’addanci.















