Babban hafsan sojojin Faransa, Janar Fabien Mandon, ya bayyana cewa Amurka na zama aboki “mai wahalar hasashe,” yana mai sukar yadda Washington ta shiga rikici da Iran ba tare da tuntubar kawayenta ba. Ya ce duk da cewa dangantakar kasashen biyu na da ƙarfi, irin wannan mataki yana shafar tsaro da muradun Faransa kai tsaye.
Janar Mandon ya kwatanta wannan da janyewar Amurka daga Afghanistan, wanda shi ma ya ce an yi shi ba tare da shawarar abokan hulɗa ba. Ya kara da cewa sojojin Faransa sun tilasta yin gaggawar daukar matakai domin kare ‘yan kasarsu da muradunsu a yankin Gabas ta Tsakiya. Haka kuma, jami’a a ma’aikatar tsaro Alice Rufo ta jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin kawaye, musamman wajen kare fararen hula da sojojin da ke aiki a waje.
Ta kuma nuna cewa rikicin ya riga ya shafi Faransa kai tsaye, inda aka samu asarar rayuka da jikkata wasu daga cikin sojojinta a yankin. A wajen taron dabarun tsaro da aka gudanar a Paris, an tattauna yadda sabbin rikice-rikice ke sauya yanayin yaki, ciki har da karuwar hare-hare ta yanar gizo, sararin samaniya da makamashi.
A halin yanzu, rikicin da ya fara bayan hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran ya bazu zuwa kasashe da dama, tare da jawo mummunan tasiri ga fararen hula. Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane miliyan guda sun tsere zuwa Lebanon, ciki har da dubban yara, yayin da hare-haren suka lalata gidaje da asibitoci. Rahotanni sun kuma nuna cewa mutane fiye da 900 sun mutu, yayin da sama da 2,200 suka jikkata sakamakon tashin hankalin.







