An rufe filin jirgin sama na LaGuardia da ke New York a daren Lahadi bayan wani jirgi ya yi karo da motar kashe gobara, lamarin da ya jawo mace-mace da jikkata, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Amurka (FAA) ta sanar da dakatar da duk tashin jirage daga filin, tare da bayyana cewa za a ci gaba da rufe shi har zuwa karfe 18:00 GMT. Sai dai ana ganin akwai yiwuwar a tsawaita lokacin rufewar.
Har yanzu ba a fitar da cikakkun bayanai kan adadin wadanda suka mutu ko suka jikkata ba, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike kan yadda hatsarin ya faru.














