Wasu da ake zargin ‘yanta’addan Boko Haram da ISWAP ne sun kai hari kan wani sansanin sojojin Nijeriya a unguwar Ajilari Cross da ke wajen birnin Maiduguri a jihar Borno da tsakar daren Lahadi.
Rahotanni daga jami’an tsaro, mazauna yankin da jami’an agaji sun ce sojoji sun yi gaggawar mayar da martani tare da fatattakar maharan kafin su yi barna mai yawa. Unguwar ta koma cikin kwanciyar hankali a safiyar Litinin.
Mai magana da yawun ‘yansanda a jihar Borno, Nahum Kenneth Daso, ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun daƙile harin da ake zargin ‘yanta’addan Boko Haram ko ISWAP ne suka kai, tare da hana su cimma manufarsu.
Mazauna yankin sun ce an samu mutuwar maharan huɗu yayin arangamar, yayin da jami’an agaji suka ce ba a samu asarar rayukan fararen-hula ba.
Harin na zuwa ne yayin da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke ƙara kai hare-hare kan sansanonin sojoji a arewa maso gabashin Nijeriya, duk da cewa Maiduguri ta shafe wasu shekaru cikin kwanciyar hankali idan aka kwatanta da shekarun baya.
Tushen labari: Newstimehub














