Jagoran adawa a Uganda, Bobi Wine, ya bayyana cewa ya bar ƙasar domin gujewa abin da ya kira binciken soji bayan zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a ranar 15 ga Janairu. Wine, wanda sunansa na asali Kyagulanyi Ssentamu ne, ya shiga ɓoye nan da nan bayan zaɓen da sakamakon hukuma ya nuna cewa shugaban ƙasar Yoweri Museveni ne ya lashe da kashi 71.6% na ƙuri’u.
Jagoran adawar ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen, yana zargin cewa an tafka maguɗi da kura-kurai da dama. Tsawon makonni ba a san inda yake ba, abin da ya janyo damuwa kan lafiyarsa, musamman bayan hafsan sojin Uganda kuma ɗan shugaban ƙasa, Muhoozi Kainerugaba, ya yi wasu kalamai masu tsauri a shafinsa na sada zumunta.
A cikin wani bidiyo da ya wallafa a yanar gizo, Wine ya tabbatar da cewa ya bar Uganda domin wasu muhimman ayyuka a ƙasashen waje, amma bai bayyana inda yake ba. Ya kuma gode wa magoya bayansa da suka taimaka masa ya ɓoye yayin da yake zargin cewa hukumomi na neman sa.
Wine ya ce yana da niyyar dawowa Uganda domin ci gaba da gwagwarmayar siyasa a lokacin da ya dace. A yayin yaƙin neman zaɓe, sau da yawa ya halarci taruka yana sanye da hular kariya da rigar kariya saboda fargabar tsaro. Shi ne fitaccen ɗan takara daga cikin ‘yan adawa da suka kalubalanci Museveni, wanda ake sa ran zai sake rantsuwa karo na bakwai a watan Mayu bayan kusan shekaru hamsin yana mulki.














