Nijar Ta Nuna Fushi Ga Tarayyar Turai Kan Batun Tsare Tsohon Shugaba Bazoum

Nijar ta nuna rashin jin daɗi ga Tarayyar Turai kan ƙudurin da ya nemi a saki tsohon shugaban ƙasar Mohamed Bazoum, tana mai zargin ƙungiyar da tsoma baki cikin harkokin cikin gida.

Newstimehub

Newstimehub

13 Mar, 2026

2d852d73df590ba2424714e9ea20a00226910d466aa36444feb67e4d37da7b92 1

Ministan harkokin waje na Nijar, Bakary Yaou Sangaré, ya gayyaci jakadiyar Tarayyar Turai a ƙasar, Nicoletta Avella, zuwa ofishinsa domin nuna rashin jin daɗin gwamnatin Nijar kan ƙudurin majalisar dokokin Tarayyar Turai da ya shafi halin da tsohon shugaban ƙasar Mohamed Bazoum ke ciki.

Bayan ganawar, ministan ya miƙa mata wasiƙar koke inda gwamnatin Nijar ta yi Allah wadai da abin da ta kira tsoma bakin Tarayyar Turai cikin harkokin cikin gidan ƙasar. Gwamnatin ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wani abin da take gani a matsayin raini ko katsalandan daga ƙasashen waje ba.

Wannan martani ya biyo bayan ƙudurin da majalisar dokokin Tarayyar Turai ta amince da shi a ranar 11 ga Maris 2026, inda ta yi kira da a saki Bazoum da matarsa da sauran mutanen da aka tsare bayan juyin mulkin da ya faru a Nijar. Majalisar ta kuma bayyana damuwa kan halin tsaro da jinƙai a yankin Sahel, inda ta ce dubban mutane sun rasa matsuguni kuma miliyoyi ke buƙatar agaji.

Tsohon shugaban Nijar Mohamed Bazoum dai an hambarar da gwamnatinsa ne a juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga Yulin 2023, inda Janar Abdourahamane Tiani ya karɓi mulki. Rikicin siyasa bayan juyin mulkin ya sa Nijar tare da Mali da Burkina Faso suka fice daga ECOWAS, inda suka kafa ƙungiyar AES ta ƙasashen Sahel.

Majiyar Labari: NEWSTIMEHUB