An ji ƙarar harbe-harbe da fashewar wasu abubuwa masu ƙarfi a yankin Tahoua na Jamhuriyar Nijar a daren Lahadi, lamarin da ya tayar da hankalin mazauna yankin. Shaidu sun ce an ji karar harbe-harben da misalin ƙarfe 3:00 na dare, sannan aka ga wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun iso kan babura, inda aka yi musayar wuta a kusa da hanyar filin jirgin saman garin da kuma tsakiyar birnin.
Daga bisani dai mazauna yankin sun ce kafin wayewar gari lamarin ya lafa kuma kwanciyar hankali ya dawo. Har zuwa safiyar Litinin, ba a bayyana adadin wadanda suka mutu ko suka jikkata ba sakamakon abin da ya faru.
Yankin Tahoua dai na daga cikin wuraren da Nijar ke fama da matsalar tsaro tsawon shekaru, musamman hare-haren ƙungiyoyin ta’adda masu alaƙa da Al-Qaeda da Daesh. Har ila yau, yankin na fama da matsalar ’yan fashi da makami da kuma safarar man fetur, miyagun ƙwayoyi da magungunan jabu ta kan iyaka.
Majiyar Labari: NEWSTIMEHUB






