Kungiyar Agaji ta Red Cross ta ce hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa a Gaza, da nufin mamaye birnin a yankin Falasdinawa da aka yi wa ƙawanya abu ne da ba za a iya jurewa ba.
Babban mai magana da yawun Ƙungiyar Agaji ta Red Cross Christian Cardon ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, tsananin tashin hankali a Gaza na nufin ƙarin kashe-kashe, da rasa matsugunai, da ɓarna da kuma jawo firgici.
“Gaza wani rufaffen waje ne, wanda babu wanda zai iya tserewa daga gare shi, kuma inda babu hanyoyin samun lafiya da abinci da tsaftataccen ruwan sha,” in ji Cardon.
Isra’ila ta yi luguden wuta kan birnin Gaza da wajensa a cikin dare, kamar yadda mazauna garin suka fada a ranar Alhamis, yayin da sojoji suka sanar da daukar matakin farko a yunkurinsu na ƙwace babbar tunga ta karshe ta kungiyar Hamas.














