Gwamnatin Ghana za ta fara cin tarar direbobin da ke lodi fiye da ƙima Cedi 50,000

Gwamnatin Ghana ta ce hanyoyin ƙasar da dama sun lalace sakamakon lodi fiye da ƙima da ake yi wa motoci wanda hakan ya sa za a ƙara yawan tarar da ake cin direbobin da suka saɓa doka daga Cedi 5,000 zuwa Cedi 50,000.

Newstimehub

Newstimehub

1 Aug, 2025

b0cb0ef71a777abd4b0ad6e8aa16e05a5778fb3390bbf1982068c26160242154

Gwamnatin Ghana ta bayyana cewa za ta ɗauki matakai masu tsauri kan direbobin da ke ɗaukar kaya fiye da ƙa’idar nauyin da aka ƙayyade domin kare titunan ƙasar daga lalacewa da wuri.

Ɗaya daga cikin waɗannan matakai shi ne ƙara yawan tarar da ake cin direbobin da suka saɓa doka daga Cedi 5,000 zuwa Cedi 50,000.

Ministan Tituna na Ghana Mista Kwame Governs Agbodza ne ya bayyana hakan a yayin gabatar da jawabi a wani taro a Accra babban birnin ƙasar a ranar Laraba.

Ya bayyana cewa hanyoyin ƙasar da dama sun lalace sakamakon lodi fiye da ƙima da ake yi wa motoci.

Ministan ya bayar da misali da hanyar Takwa wadda ya ce ba ta wuce shekara guda da aka yi ta ba amma ta lalace saboda yadda ake yin lodin da ya wuce ƙima.

“Mun ba da shawarar a ƙara tsananta hukunci ga waɗanda ba za su bi doka ba su kuma ci gaba da lodin kaya fiye da ƙa’ida. Don haka za ku ga cewa za a ƙara kuɗaɗen tara da cajin da ake biya. Muna da niyyar ƙara tara daga Cedi 5,000 zuwa Cedi 50,000.” In ji Mista Agbodza.

Ya ƙara da cewa an kafa kwamitin ƙwararru daga sassa daban-daban don sake dubawa da inganta tsarin da ake bi na yi wa motoci lodi.