Ƙarar bamabamai ta rikirkita birnin Caracas bayan Trump ya sha alwashin kai hari a ƙasar Venezuela

Ƙarar bamabamai ta rikirkita birnin Caracas bayan Amurka ya ci alwashin kai hare-hare a ƙasar Venezuela, duk da yake Maduro ya musanta yin wani abu ba daidai ba sanna ya yi kira a haɗa kai.

Newstimehub

Newstimehub

3 Jan, 2026

venezuela us 38765

An ji ƙarar fashewar wasu bamabamai, tare da ƙarar jiragen sama a Caracas, babban birnin Venezuela da misalin ƙarfe 2:00 na dare (0600 GMT) ranar Asabar, kamar yadda wani ɗanjarida na kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito.

An ji waɗannan fashe-fashe ne bayan shugaban Amurka Donald Trump, ya sha alwashin kai hare-hare ta ƙasa a Venezuela. Tuni ya tura wata tawagar sojojin ruwa ƙasar wadda ke yankin Caribbea.

An ci gaba da jin ƙarar fashewar bamabamai da misalin ƙarfe 2:15 na dare, ko da yake ba a san takamaimai inda aka ji ƙarar ba.