Turkiyya ta ɗora wa Isra’ila laifin rikicin Sweida, ta yi kira ga samar da makoma mai adalci a Syria

Al shaibani, tare da Fidan, sun jaddada muhimmancin hadin kai kan tsaro da batutuwan soji don tsare iyakoki da yaki da ta’addanci.

Newstimehub

Newstimehub

13 Aug, 2025

b690b5db5ce1ab62e8ffb6f9967cadd1a9e698b421489e89fa93c3155ab09918

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya soki rawar da Isra’ila ke takawa a rikicin baya-bayan nan a garin Sweida na kasar Syria, inda ya bayyana damuwar Turkiyya game da tsoma bakin kasashen waje kan harkokin Syria.

“Daya daga cikin manyan masu taka rawa a bayan wannan bakin hoto (na al’amuran Sweida) ita ce Isra’ila,” in ji Fidan yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Ministan Harkokin wajen Syria Asaad Hassan al Shaibani a Ankara ranar Larabar nan.

Ya kuma jaddada manufar Turkiyya game da Syria bayan rikici, yana mai cewa: “Ya kamata sabuwar Syria ta zama Syria da dukkanin al’ummomi, akidu, da al’adu ke samun kariya, kuma za su iya rayuwa tare.

“A matsayinmu na Turkiyya, muna bayar da shawarwarinmu ta wannan mahanga.”

Fidan ya yi gargadin cewa Ankara na shaida abubuwan da ba za ta iya jure kallon su haka kawai ba.

Ya ce, “’yan ta’addar YPG ba su bar Syria ba, bai kamata su yi tunanin ba ma ganin haka.”

Ministan ya yi kira ga kungiyar YPG da ta gaggauta kawo karshen barazanar da take yi wa Turkiyya da kuma yankin, inda ya bukaci su da mayakansu da suka dakko daga kasashen waje da su fice daga yankin Syria ba tare da bata lokaci ba.

Ministan harkokin wajen Syria Asaad al Shaibani ya bayyana yadda kasashen ketare ke ci gaba da shiga tsakani a kasar ta Syria, yana mai bayyana wasu a matsayin “masu aiki kai tsaye da kuma neman raunana kasar ta Syria da haifar da wanzuwar wata kasa mai rauni”.

Ya kuma ce al’ummar Druze har yanzu wani bangare ne na al’umar Syria, yana mai watsi da ikirarin Isra’ila da ke nuna akasin haka.