Turkiyya, Sifaniya, Birtaniya da Jamus sun yi tir da faɗaɗa matsugunan da Isra’ila ke yi a yankin E1

Ma’aikatun harkokin wajen ƙasashen sun yi gargaɗin cewa sabon aikin da Isra’ila za ta yi zai raba kan Yammacin Kogin Jordan, tare da keɓe Gabashin Birnin Ƙudus da kuma barazana ga tsarin samar da ƙasashe biyu.

Newstimehub

Newstimehub

15 Aug, 2025

e8aa49f7660bee08186c75e988c625673b8865e2451a48945aa0bc4fcc904fa7

Ƙasashen Turkiyya da Sifaniya da Birtaniya da kuma Jamus sun yi Allah wadai da amincewar da Isra’ila ta yi ta samar da sabbin matsugunai ba bisa ka’ida ba a yankin E1 wato Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye, suna masu gargaɗin cewa hakan zai kawo cikas ga tsarin samar da ƙasashe biyu da kuma keta dokoƙin ƙasa da ƙasa.

A ranar Alhamis, kafofin yaɗa labaran Isra’ila suka ba da rahoton cewa Ministan Kuɗi na ƙasar Bezalel Smotrich ya amince da gina matsugunan mutane 3,401 a Ma’ale Adumim da ke Gabashin Birnin Ƙudus, da kuma wasu 3,515 a yankunan da ke kewaye.

Aikin dai na da nufin raba Yammacin Kogin Jordan zuwa arewaci da kudancin ƙasar, tare da mayar da Gabashin Birnin Ƙudus saniyar ware.

Ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta ce matakin ya yi watsi da dokoƙin ƙasa da ƙasa da kuma ƙudurorin Majalisar Ɗinkin Duniya sannan hakan “na nufin take ‘yancin samar da ƙasar Falasɗinu, da manufar samar da ƙasashe biyu, da kuma fatan da ake da shi na samun zaman lafiya mai ɗorewa.”

Kazalika, ma’aikatar ta sake jadadda goyon bayan Turkiyya ga ƙasar Falasdinu mai cin gashin kanta bisa kuɗurin yarjejeniyar iyakoki na 1967 da kuma Gabashin Ƙudus a matsayin babban birninta.

Ministan Harkokin Wajen Sipaniya Jose Manuel Albares ya kira faɗaɗa yankin da wani “sabon saba dokokin ƙasa da ƙasa” wanda “ya gurgunta yiwuwar samar da zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu wanda ke zama hanya daya tilo ta zaman lafiya,” tare da yin Allah wadai kan tashe-tashen hankula na raba matsugunai.