Turkiyya ta samu nasarar gwajin wani sabon nau’in jirgi maras matuƙi mai suna Simsek, wanda ke da tsananin sauri, kamar yadda wani babban jami’in tsaro ya bayyana.
Jirgin wanda ake harbawa kamar roka, ya tashi daga ƙasa a karon farko, kuma za a iya amfani da shi a matsayin jirgi domin kai hari da kuma wurin kai harin ƙunar baƙin-wake, in ji Haluk Gorgun, shugaban Ma’aikatar Masana’antar Tsaro ta Turkiyya, a dandalin sada zumunta na Turkiyya, NSosyal.
“Masana’antar tsaronmu ta ƙara wani muhimmin fasaha a cikin kayan aikinta,” ya rubuta.