Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa rundunar sojin Amurka ta kai wani babban hari a Kharg Island na ƙasar Iran. Ya ce farmakin ya lalata muhimman wuraren soji a tsibirin, amma ya jaddada cewa Amurka ba ta kai hari kan wuraren mai ba a wannan lokaci.
Trump ya kuma yi gargaɗin cewa idan Iran ko wani bangare ya ci gaba da kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen ruwa a Strait of Hormuz, Amurka na iya kai hari kan wuraren mai na Iran. Ya ce matakin zai iya canzawa nan take idan an ci gaba da barazana ga wucewar jiragen ruwa cikin aminci a mashigar.
Tsibirin Kharg na da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin Iran, domin kusan kashi 90% na fitar ɗanyen man ƙasar na bi ta wurin. Tsibirin yana kusan kilomita 30 daga gabar Iran, kuma masana na ganin duk wani hari a wurin na iya haifar da gagarumin tasiri ga kasuwar mai ta duniya.
A halin yanzu rikicin ya sa zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigin Hormuz ta ragu, yayin da Amurka ke shirin fara rakiyar jiragen dakon mai ta hanyar rundunar sojin ruwanta domin dawo da zirga-zirgar mai da kuma rage hauhawar farashin mai a Amurka.














