Shugaban Amurka Donald Trump ya ce tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha za ta iya taimaka masa wajen shiga aljanna, yana mai yin barkwanci cewa damar samun makoma mai kyau a halin yanzu ba ta da yawa.
“Ina so na yi koƙari domin na shiga aljanna idan hakan zai yiwu” kamar yadda Trump ya shaida wa shirin safe na Fox News “Fox & Friends.”
“Na amince cewa ba na yin abu mai kyau – ina ji a jikina cewa na kusa zuwa kabarina! Amma idan na samu zuwa aljanna, wannan zai zama ɗaya daga cikin dalilai.”
A baya dai shugaban, mai shekaru 79, ya sha alwashin kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine da kuma fatansa na lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya.
Kalamansa na baya bayan nan sun nuna sha’awarsa ta tafiya lahira fiye da zaman duniya.
Trump shi ne shugaban Amurka na farko da aka yanke masa hukunci laifi, wanda ya samo asali daga yunƙurin ba da cin hanci ga wata babbar ‘yar wasan kwaikwayo.
Sau biyu ana tsige shi, kana ya sha shiga badaƙala a rayuwarsa.
‘Ceto daga Allah ‘