Tsohon ɗan wasan Arsenal ɗan asalin Ghana, Thomas Partey ya rattaba hannu kan kwantiragi da Villarreal ta Sifaniya bayan barin Arsenal a ƙarshen kakar bara.
Partey ya koma ne a matsayin kyauta, saboda kwantiraginsa da Arsenal ta ƙare wa’adi ba tare da wani kulob ya saye shi ba. Kwantiragin ta shekara guda ce tare da zaɓin ƙarin watanni 12.
Ɗan wasan mai shekaru 32 zai bar Ingila, inda a aka fara yi masa shari’a kan zargin fyaɗe da wasu mata uka suka masa.