Shugaban Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijirar Falasɗinu (UNRWA) ya bayyana cewa tsarin rarraba tallafin da ake yi a Gaza a halin yanzu yana ƙarƙashin kulawar wasu sojojin haya, daga ciki har da wasu da ya kira “tantirai maƙiya Musulunci.
Philippe Lazzarini ya jaddada cewa magance yunwa a Gaza “na buƙatar samun damar kai tallafi ba tare da tsangwama ba, a cikin yanayi mai aminci da kuma a duk inda ake buƙata.”
“Majalisar Ɗinkin Duniya, ciki har da UNRWA da abokan hulɗa, suna da kayan aiki da ƙwarewa. Ku bar mu mu yi aikinmu,” in ji shi.
Tun daga ranar 27 ga Mayu, Isra’ila ta kafa wata hanyar rarraba tallafi ta daban ta hanyar abin da ake kira Gaza Humanitarian Foundation, wanda Amurka ke goyon baya amma Majalisar Dinkin Duniya da Falasɗinawa suka ƙi amincewa da ita, suna kiranta da “tarkon mutuwa.”














