Sojojin Pakistan sun kashe ‘yan ta’adda 50 a kan iyakar Afghanistan: Sanarwa

Rundunar sojin Pakistan ta ce ta ƙaddamar da samame ne a kan iyakar ƙasar da maƙwabciyarta Afghanistan domin fatattakar ‘yan ta’adda da ‘yan a-ware.

Newstimehub

Newstimehub

12 Aug, 2025

1754977620604 q0db88 41d655791d94bd036e55452092c9f3e61b648bcaee91220fc5bdbf7ac5f5362e

Rundunar Sojin Pakistan ta sanar a ranar Talata cewa ta kashe ‘yan ta’adda 50 a kan iyaka da maƙwabciyarta Afghanistan a cikin kwanaki huɗu, a wani yanki mai cike da tashin hankali a kudu maso yammacin ƙasar da ke da wasu muhimman ayyukan more rayuwa na ƙasar China.

An kashe ‘yan ta’addan ne a wani samame da aka ƙaddamar a ranar Alhamis, a cewar sanarwar da rundunar sojin ta fitar a Balochistan, inda ‘yan ta’adda da ‘yan a-ware ke gudanar da ayyukansu.