Sojojin Sudan sun faɗa a ranar Lahadi cewa sun kashe gomman mayaƙan sa-kai na Rapid Support Forces (RSF) kuma sun hallaka motocin yaƙi 141 a hare-haren da suka kai a faɗin ƙasar a wannan watan.
Sojojin da abokan ƙawance su na ci gaba da gudanar da ayyukan soji a kan “RSF da mayaƙansu na haya”, a fannoni daban-daban, in ji sojin a wata sanarwa a dandalin sada zumunta na X.
Ayyukan soji tsakanin 1 zuwa 14 ga Yuni sun jawo “asara mai yawa” ga RSF, ciki har da lalata motocin yaki, ma’ajiyoyin makamai, da kayayyakin soja, in ji sanarwar.
A yankin Darfur, sojin sun ce sun lalata motocin yaki 29 na RSF kuma sun kashe ‘yan tawayen da yawa.
An harbo jirgi mara matuki na RSF
Har ila yau, ta ba da rahoton lalata wurare da dama a birnin Nyala, ciki har da ma’ajiyoyin bam guda biyu, da wuraren ajiye kayan aikin soja guda biyu, da wuraren ajiyar bama-baman jiragen marasa matuka guda biyu, da babbar ma’ajiyar mai da ake amfani da shi wajen tallafawa ayyukan RSF.
A yankin Kordofan, sojin sun ce sun lalata motocin yaki 91 kuma sun kashe mambobin RSF da yawa.
A Jihar White Nile, rundunar sojin ta ce ta harbo wani jirgi mara matuki na RSF a birnin Kenana.
A Jihar Blue Nile, sojin sun ba da rahoton lalata motocin yaki 21 tare da haifar wa sojoji da kayan aikin RSF mummunar asara.
Mummunan yaƙi
Sojin sun ce an lalata jumullar motocin yaƙi guda 141 a lokacin da aka bayar da rahoton, yayin da aka kuma kwace adadi mai yawa na makamai, da bama-bamai, da kayan aikin soja.
“Ayyukan za su ci gaba har sai an kawar da RSF kuma an dawo da tsaro da zaman lafiya a faɗin ƙasar,” in ji sanarwar.
Har yanzu RSF ba ta yi tsokaci kan sanarwar sojin ba.
Sudan ta kasance cikin rikici tun Afrilu 2023, lokacin da aka fara samun saɓani tsakanin soji da RSF kan shirin haɗe sojojin sa-kai da sojin ƙasar. Wannan yaƙi ya janyo ɗaya daga mafi munanan mastalar jinƙai a duniya, inda dubban mutane suka mutu kuma kusan miliyan 13 suka rasa matsugunnesu.















