Masana harkokin siyasa a Nijeriya sun fara tofa albarkacin bakinsu dangane da dacewa ko rashin dacewa bayan wasu sabbin jam’iyyu guda 171 sun gabatar da bukatar neman a yi musu rijista a Hukumar Zabe ta Kasar (INEC).
Wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Ilmantar da Masu Kada Kuri’a na INEC, Sam Olumekun ya fitar ta ce an wallafa duka sunayen sabbin jam’iyyu da suke neman rijista a shafin intanet din hukumar.
Ya ce zuwa ranar Laraba 3 ga watan Satumban bana, akwai jimillar jam’iyyu 171 da suke neman rijista.
Farfesa Kamilu Sani Fagge na tsangayar nazarin siyasa a Jami’ar Bayero ta Kano ya shaida wa TRT Afrika cewa akwai alfanu da rashin alfanun jam’iyyu barkatai a siyasar ƙasa.
Ya ce wadanan kungiyoyi da suke neman a yi musu rijista suna da ’yancin neman hakan a doka.
Malamin jami’ar ya ce bayar da dama a samu jam’iyyu da yawa yana bai wa jama’a damar tsayawa takara kuma a ɗaya ɓangaren yana ba su damar zabar ’yan takarar da suke so.
Ko da yake wasu masana suna ganin hakan yana tattare da wasu ƙalubale saboda suna cewa hatta wajen gudanar zabe kudin da za a kashe zai yi yawa sosai saboda yawan jam’iyyu musamman ta fuskar ƙara yawan kayayyakin zaɓen da za a buƙata.
Idan za a tuna a shekarar 2020, hukumar zaben kasar ta soke rijistar wasu jam’iyyu 74 saboda ko dai sun kasa cin ko da kujera daya a shekarar 2019, ko kuma ba su cike wasu tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Nijeriya ba.
Sakamakon haka ne ya sa jam’iyyu 18 kawai suka iya fafatawa a zaben shekarar 2023.
Farfesa Kamilu ya ce idan jam’iyyu suka kai har guda 171, to gaskiya za a samu galibin jam’iyyun na je-ka-na-yi-ka ne.