Rundunar sojin Nijeriya ta yi sabbin naɗe-naɗe

Babban hafsan sojojin ƙasar ya umarci hafsoshin da aka naɗa su ruɓanya ƙoƙarinsu wajen ci gaba da kai kan ‘yan ta’addan da sauran matsalolin tsaro.

Newstimehub

Newstimehub

18 Aug, 2025

492351352 1000598715528171 5624130680939351907 n

Babban hafsan sojojin ƙasan Nijeriya, Lutanan Janar Olufemi Oluyede ya amince da sabbin naɗe-naɗe da sauye-sauye kan muhimman muƙamai cikin rundunar sojin ƙasar.

Wata sanarwar da muƙaddashiyar daraktar watsa labaran rundunar sojin ƙasar, Appolonia Anele, ta fitar ranar Lahadi ce ta bayyana wannan a birnin Abuja.

Anele ta ce sabbin naɗe-naɗen sun shafi manyan jami’ai ne a hedikwatar sojin da kuma manyan rundunonin soji da kwamandojin cibiyoyin bayar da horo da sauransu.

Ta ce an naɗa Manjo-Janar Adekunle Adeyinka a matsayin babban jami’in da ke kula da sufiri inda Manjo Janar A.A. Adekeye ya zama babban jami’in da ke kula da ma’aikata, kuma Manjo Janar T.B. Ugiagbe ya zama babban jami’i mai kula da daidaito da gwaji.

Ta ƙara da cewa an naɗa Manjo Janar A.A. Idris a matsayin babban jami’in sojin da ke kula da tattara bayanan asiri; kuma aka naɗa Manjo Janar M.O. Erebulu a matsayin shugaban ‘yan sandan sojin.

“Sauran sun haɗa da Manjo Janar  E.A. Anaryu a matsayin kwamandan da ke kula da harkar sufuri da Manjo Janar J.E. Osifo a matsayin babban Daraktan  Hukumar Kuɗi ta rundunar Sojojin Nijeriya.

“An naɗa manjo Janar S.A. Akesode a matsayin shugaban rundunar tabbatar da zaman lafiyar Tarayyar Afirka a Tigray, Ethiopia.