Hukumomi da masana tattalin arziki a ƙasashe daban-daban na Africa sun yi gargaɗi cewa tashin gwauron zabi na farashin mai sakamakon rikicin Iran na iya jefa tattalin arzikin yankin cikin matsala.
Sun ce hauhawar farashin mai na iya shafar tsarin hada-hadar kuɗi da manyan sassa na tattalin arziki kamar hakar ma’adanai, lamarin da zai iya kawo cikas ga farfaɗowar tattalin arzikin ƙasashen nahiyar.
A watannin baya, manyan bankunan ƙasashe da dama sun fara rage kuɗin ruwa domin tallafa wa tattalin arziki bayan raguwar hauhawar farashi da kuma samun daidaito a kasuwar musayar kuɗi. S
ai dai rikicin Gabas ta Tsakiya na iya sa a dakatar da waɗannan tsare-tsare. Bank of Uganda ya ce hauhawar rashin tabbas a tattalin arzikin duniya na ƙara jefa bankunan ƙasashe cikin ƙalubale.
Haka kuma Banco Nacional de Angola ya dakatar da shirin rage kuɗin ruwa bayan ragi uku da aka yi a baya.
Gwamnan bankin, Manuel Tiago Dias, ya ce yiwuwar tsawaita rikicin Gabas ta Tsakiya na iya shafar hanyoyin jigilar kayayyaki da kuma samar da kayan aikin gona da takin zamani.
Masana sun ce wasu ƙasashe kamar Ghana, Nigeria, Zambia da Kenya na iya sake duba tsare-tsarensu na kuɗi. A halin yanzu, farashin ɗanyen mai na Brent ya kusanci dala 100 a kowace ganga, bayan ya kai kusan dala 120 a farkon makon, lamarin da masana ke ganin zai iya rage darajar kuɗaɗen wasu ƙasashen Afirka idan ya ci gaba.














