Ranar Iya Karatu ta Duniya: Mutum 13,132 cikin 18,741 sun iya karatu a Jamhuriyar Nijar —Minista

Dakta Elisabeth Shérif ta ce wannan sakamakon ya samu ne sakamakon matakan da shugabannin Nijar suka ɗauka waɗanda suka kamata a yabawa.

Newstimehub

Newstimehub

8 Sep, 2025

tiani signature

A Jamhuriyar Nijar shirin wayar da kan jama’a na shekarar 2025 kan iya karatu ya kai ga mutum 24,573, ciki har da mata 19,619, inda aka gwada mutum 18,741 a cikinsu kuma aka tabbatar da cewa mutum 13,132 sun iya karatu, wato kashi 70.07 cikin 100 ke nan.

 Kamfanin dillancin labaran ƙasar ANP ya ruwaito cewa Ministar Ilimin ƙasar Dakta Élisabeth Shérif ce ta bayyana hakan ranar Lahadi a jawabin da ta yi albarkacin Ranar Iya Karatu ta Duniya.

 Dakta Elisabeth Shérif ta ce wannan sakamakon ya samu ne sakamakon matakan da shugabannin Nijar suka ɗauka waɗanda suka kamata a yabawa.

Ta ce bisa ga nauyin da Shugaban ƙasar Janar Abdourahamane Tiani ya ɗora mata, “an yi muhimman gyare-gyare kuma duk da ƙalubale iri-iri da ke fuskantar ƙasarmu, ana ci gaba da ƙara kasafin kuɗin da ake ware wa wannan batu domin amfani da iya karatu da shirin ilimin yaƙi da jahilci wajen magance matsalolin ɓangarori daban daban wajen samar da al’umma mai ƙarin adalci da ilimi da za ta iya tunkarar ƙalubalen ci-gaba.”