An gurfanar da ƙarin mutum 17 bayan tuhumar 33 bisa zargin kisan Malamar Islamiyya a Kaduna

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu a ranar 25 ga Yuni, 2026.
27 Jun, 2026
Sojojin Nijeriya sun ceto fararen-hula 53 tare da ƙwato motoci takwas a Borno

Dakarun sojin Nijeriya sun samu nasarar ceto fararen-hular bayan sun tarwatsa wani shinge da ‘yanta’adda suka kafa a Hanyar Buratai zuwa Kamuya a Jihar Borno.
26 Jun, 2026
Mutum aƙalla takwas sun mutu, an ceto 26 bayan bene mai hawa uku ya rushe a Legas

Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) ta bayyana cewa jami’an ba da agajin gaggawa sun samo gawarwaki takwas kuma sun ceto mutum 26 daga ɓaraguzan ginin zuwa misalin ƙarfe 4:20 na yammacin ranar Alhamis.
26 Jun, 2026
Kotu a Nijeriya ta yanke wa mutum uku hukuncin kisa ta rataya, ciki har da wani ɗan ƙasar waje

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama su ne a ranar 13 ga Yunin 2025 ta hannun sashenta na yaƙi da ta’addanci, bisa zarginsu da hannu a ayyukan safarar makamai da ta’addanci da suka shafi ƙetare iyakoki.
24 Jun, 2026

CBN ya ƙaddamar da jakadun kare martabar naira a ƙasar

Mutum 20 sun mutu a wani hari da aka kai a Jihar Filato a Nijeriya – ‘Yansanda

NAHCON ta kammala jigilar alhazan Nijeriya na 2026, ta soma shirye-shiryen Hajjin 2027

‘Yansandan sun fara kama waɗanda ake zargi da kisan gillar da aka yi wa wata mata a jihar Kaduna

Dakaru sun kassara ‘yanta’adda da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su a samame a Sokoto da Katsina
21 Jun, 2026
‘Yanta’adda sun kashe manoman 11 a arewa maso gabashin Nijeriya
‘Yanta’addan sun tattara manoma bakwai a ranar Asabar a ƙauyen Kuwawu da ke jihar Borno sannan suka yi musu yankar rago, kamar yadda ‘yan bijilanti na yankin suka shaida.

21 Jun, 2026
Gwamna Biodun Oyebanji na jam’iyyar APC ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Ekiti a karo na biyu
Sakamakon ya nuna cewa gwamnan ya samu nasarar ne a karo na biyu da kuri’u 319,224, inda ya doke sauran abokar takararsa na jam’iyyun PDP da ADC da suke bin bayansa.

20 Jun, 2026
Ana gudanar da zaɓen gwamna a Jihar Ekiti da ke kudancin Nijeriya
Yayin da gwamna mai ci, Biodun Oyebanji, ke neman wa’adi na biyu, ana kallon zaɓen a matsayin wani gwaji na ƙarfin jam’iyyun siyasar ƙasar gabanin babban zaɓen Nijeriya mai zuwa.

19 Jun, 2026
Rashin hukunta masu laifi na ƙara haifar da zarge-zargen kisan kare-dangi a Nijeriya: MDD
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Nazila Ghanea, wakiliya ta musamman ta Majalisar Ɗinkin Duniya kan ’Yancin Addini ko Imani, bayan wata ziyarar bincike ta makonni biyu da ta kai Nijeriya.

19 Jun, 2026
Tsoffin janar-janar a Nijeriya sun nemi a yi wa harkar tsaro garambawul bayan rasuwar Rabe Abubakar
Tsoffin manyan sojojin sun yi kira da a ƙarfafa hukumomin tsaro da inganta haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro da inganta tattara bayana sirri da kula da kan iyakoki domin rage kwararar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

17 Jun, 2026
Sojojin Nijeriya sun ceto mutum hudu da aka sace daga gungun ‘yanta’adda a Katsina
Sai dai kwamishinan ya bayyana cewa mutanen sun samu raunukan bindiga yayin da suke tsare, amma an fara ba su kulawar lafiya nan-take bayan ceton su.

17 Jun, 2026
Shugaba Tinubu ya amince a ɗauki jami’an kare daji 1,000 a Jihar Katsina
Lamarin na zuwa ne yayin da jihar Katsina da ke arewa maso yamacin ƙasar ke ci gaba da fama da fashin daji da garkuwa da mutane da sace shanu.

17 Jun, 2026
Kotu ta umarci a dakatar da aiwatar da hukuncin soke rijistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu
Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta Nijeriya ta bayyana hukuncin Babbar Kotun a matsayin tsabar rashin mutunci a harkar shari’a, tana mai cewa alƙalin ya yi biris da umarnin da kotun ta sama ta bayar tun da farko.

17 Jun, 2026
Nijeriya ta kama mutane takwas saboda yaɗa labarai marasa tushe
Gwamnatin Nijeriya ta kama aƙalla mutane takwas a ‘yan makonnin nan saboda yaɗa labaran ƙarya a kafofin sada zumunta.

16 Jun, 2026
Bankin Duniya ya ayyana tashoshin jiragen ruwan Apapa da Tincan cikin 20 da suka fi inganci a duniya
A cikin rahotonsa na yanayin aiki da kontena (CPPI) na shekarar 2025, Bankin Duniya ya lissafa tashoshin jiragen ruwa na Tincan Island da na Apapa a cikin tashoshi 20 waɗanda suka sake inganta.



