Nijeriya za ta bude manyan masana’antun sarrafa ma’adanin lithium

Masana’antun, waɗanda akasarin masu zuba jari daga China ne za su kafa, za su iya taimakawa wajen haɓaka ɗimbin arzikin ma’adinan Nijeriya zuwa ga samar da ayyukan yi a faɗin ƙasar.

Newstimehub

Newstimehub

26 May, 2025

de843ac9 a074 4999 82fd c51270bf1232

Nijeriya na shirin ƙaddamar da wasu manyan masana’antun sarrafa ma’adanin lithium guda biyu a wannan shekara, kamar yadda ministan ma’adinai na kasar ya bayyana a ranar Lahadi, hakan na nuna wani sauyi da za a samu daga fitar da ainihin ma’adinai zuwa ga ƙara masa daraja a cikin gida.

Masana’antun, waɗanda akasarin masu zuba jari daga China ne za su kafa, za su taimaka wajen mayar da ɗimbin arzikin ma’adinai da Najeriya ke da shi zuwa ga samar da ayyukan yi, da fasaha, da kuma bunƙasar masana’antu na cikin ƙasar.

Ministan ma’adinai na Nijeriya, Dele Alake ya ce, ana sa ran kamfanin sarrafa lithium da ya kai na dala miliyan 600 wanda ke kusa da kan iyakar johohin Kaduna da Neja zai fara aiki a wannan watan, yayin da ake dab da kammala aikin masana’antar sarrafa lithium wadda ta kai dala miliyan 200 da ke wajen Abuja.

Ministan ya ce ana sa ran ƙarin wasu masana’antun guda biyu a jihar Nasarawa wadda ke da iyaka da babban birnin tarayya Abuja, kafin karshen shekarar 2025.

“Yanzu muna mayar da hankali ne wajen mayar da arzikin ma’adinanmu zuwa ga darajar tattalin arzikinmu na cikin gida da samar ayyuka yi da fasaha, da kuma masana’antu,” in ji Alake.

Faɗaɗa gyare-gyaren haƙar ma’adinai a Nijeriya

Bisa ga wasu sanarwa daban-daban da gwamnonin jihohin da masana’atun suke, sama da kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen da aka kafa su sun fito ne daga ƙasar China, ciki har da kamfanin hakar ma’adinai na Jiuling Lithium da Canmax Technologies.

Sauran hannayen jarin kuma mallakin kamfanin Three Crown Mines ne na cikin gida.

Yunƙurin samar da masana’atar sarrafa ma’adanin na cikin gida ya biyo bayan wani bincike da hukumar kula da yanayin ƙasa ta Nijeriya ta gudanar a shekarar 2022, wanda ya gano tarin ma’adinin lithium mai daraja a kusan rabin jihohin da ke kasar, wanda ya jawo hankulan ƙasashen duniya.

Waɗannan ci-gaban wani bangare ne na faɗaɗa sauye-sauyen da Nijeriya ke yi a ɓangaren hako ma’adinai da aka bari a baya, wanda a halin yanzu ke ba da gudummawar ƙasa da kashi ɗaya cikin ɗari na yawan kuɗaɗne da ƙasar ke samu.    

Sauran gyare-gyaren da aka sa a gaba sun haɗa da takaita fitar da ma’adanai da ba a sarrafa su ba zuwa kasashen waje, da kuma tsara ayyukan haƙo ma’adanan, wadanda ke samar da mafi yawan ayyukan hannu da ake yi a halin yanzu, tare da kafa kamfanonin haƙar ma’adinai na jiha inda masu zuba jari za su mallaki hannun jari har kashi 75%.